Hajjin Bana: Daga Karshe NAHCON Ta Bayyana Adadin Maniyyatan da Za Su Sauke Farali

Hajjin Bana: Daga Karshe NAHCON Ta Bayyana Adadin Maniyyatan da Za Su Sauke Farali

  • Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta yi ƙarin haske kan shirye-shiryenta dangane da aikin Hajjin bana na shekarar 2024
  • Hukumar ta bayyana cewa a wannan shekarar maniyyata mutum 50,000 za su sauke farali a ƙasa mai tsarki
  • Shugaban hukumar, Malam Jalal Arabi, shi ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a birnnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ce aƙalla maniyyatan Najeriya 50,000 ne za su yi aikin Hajjin bana na 2024 a ƙasar Saudiyya.

Shugaban hukumar NAHCON, Jalal Arabi, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Hajj House ranar Juma’a a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Hajjin 2024: Gwamnan Arewa ya bai wa mahajjata tallafin maƙudan kuɗi bayan an yi ƙarin N1.9m

Hukumar NAHCON
NAHCON ta ce sama da maniyyata 50,000 za su sauke farali Hoto: AHMAD AL-RUBAYE
Asali: Getty Images

Arabi ya ce hukumar na kan shirin gudanar da aikin Hajjin cikin nasara, duk kuwa da ƙalubalen da ake fuskanta, rahoton PRNigeria ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Shirye-shiryen Hajjin bana na ɗaya daga cikin mafi wahala kuma na musamman.
"Kun san cewa a baya, muna da isasshen lokacin da za mu tsara komai a yadda muke so, amma a wannan karon, Saudiyya ta zo da lokacin da za mu yi aiki da shi.

Wane tallafi NAHCON ta samu?

Malam Arabi ya ce gwamnatin tarayya ta bada tallafi ta hanyoyi da dama, musammnan ta hanyar kawo tsare-tsare da za su taimaki hukumar domin tabbatar da cewa komai ya tafi daidai ba tare da wata tangarɗa ba.

Shugaban hukumar ta NAHCON ya yi nuni da cewa, yanzu hukumar a gaba ta san hanyar da ya fi dacewa ta bi domin gudanar da al'amuranta.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa matashi ɗan shekara 36 a babban muƙami, ya faɗi wasu kalamai

Ya bada tabbacin cewa hukumar za ta riƙa faɗakarwa tare da wayar da kai domin tabbatar da cewa maniyyata sun fuskanci inda aka dosa.

Ma'aikatar Hajji da Umrah ta ƙasar Saudiyya dai ta ware kujerun Hajji 95,000 ga Najeriya domin aikin Hajjin bana na shekarar 2024.

NAHCON ta ƙara kuɗin Hajji

A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da ƙarin kuɗin zuwa aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya na shekarar 1445 (2024).

Hukumar ta ƙara naira miliyan 1.9 ga maniyyata masu son zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel