Dattawan Arewa Sun Fadi Babbar Nadamar da Yankin Ya Yi Kan Zaben Shugaba Bola Tinubu

Dattawan Arewa Sun Fadi Babbar Nadamar da Yankin Ya Yi Kan Zaben Shugaba Bola Tinubu

  • Ƴan watanni bayan hawan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan mulki, ƙungiyar NEF ta ce yankin Arewa ya yi nadamar zaɓensa
  • Kakakin ƙungiyar ya bayyana cewa yankin ya fahimci ya yi kuskure kan yadda ya yi wa Shugaba Tinubu ruwan ƙuri'u
  • Ya yi nuni da cewa nan gaba yankin zai sabuwar hanya wajen zaɓen ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar dattawan Arewa (NEF) ta nuna nadamarta kan yadda yankin ya kaɗa ƙuri'u masu yawa ga Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023.

A cikin ƴan takara uku da ke kan gaba a zaɓen shugaban kasa na 2023, Tinubu, wanda ya tsaya takara a jam’iyyar APC, ya samu mafi yawan ƙuri’u daga yankin.

Kara karanta wannan

"Makaho ne kaɗai zai ce Tinubu ya gaza" Minista ya maida zazzafan martani ga NEF

NEF ta yi nadamar zaben Tinubu
An dade ana sukar salon mulkin Shugaba Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

A wata hira da jaridar The Guardian a ranar Talata, Abdul-Azeez Suleiman, mai magana da yawun ƙungiyar, ya ce nan gaba yankin zai sake lale wajen zaɓar ɗan takara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace sabuwar hanya Arewa za ta bi?

Kakakin na ƙungiyar dattawan Arewa ya bayyana cewa yankin Arewa zai bada fifiko kan haɗin kai da fahimtar juna wajen zaɓar ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa.

A kalamansa:

"Arewa ta yi kuskure wajen zaɓen Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa a 2023, kuma da wuya su sake maimaita irin kuskuren nan gaba.”
“Sun koyi darasi daga kuskuren da suka yi a baya kuma za su yi ƙoƙarin zaɓo ɗan takarar da zai iya haɗa kan ƙasar nan tare da gudanar da mulki domin amfanin ƴan Najeriya baki ɗaya."
"A gaba, Arewa za ta yi taka-tsan-tsan wajen zaɓar ɗan takarar shugaban ƙasa. Za su ba da fifiko ga wanda ake ganin ya fi kowa karɓuwa, ba ya da cece-kuce, wanda ke a shirye domin kare muradun kowane yanki na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya caccaki dattawan Arewa kan kalaman da suka yi game da Bola Tinubu

"Kuskuren goyon bayan Tinubu a 2023 ya koya musu muhimmancin haɗin kai da fahimtar juna wajen zaɓar ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa."

Atiku ya shawarci Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya yi tir da yadda gwamnatin Najeriya ta tashi kuɗin lantarki.

Jagoran ƴan adawan na ƙasar nan ya ce dole a bi a hankali, a kawo tsare-tsaren da za su takaita wahalar da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel