Tinubu Ya Yi Alkawarin Rage Farashin Man Fetur Zuwa N100? Gaskiya Ta Bayyana

Tinubu Ya Yi Alkawarin Rage Farashin Man Fetur Zuwa N100? Gaskiya Ta Bayyana

  • An ga shugaban ƙasa Bola Tinubu a wani faifan bidiyo yana cewa zai rage farashin man fetur zuwa Naira 100
  • Sai dai an gudanar da bincike kan bidiyon, inda aka gano cewa na ƙarya ne kuma sauya shi aka yi
  • Wasu ƴan Najeriya sun mayar da martani kan bidiyon, inda suka bayyana shi a matsayin ƙarya, yayin da wasu suka amince da sahihancinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wani dandalin binciken gaskiya ya yi bincike kan wani faifan bidiyo da ke nuna shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi alƙawarin rage farashin man fetur zuwa Naira 100.

Wani mai amfani da X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) ne ya sanya bidiyon mai iƙirarin rage farashin mai wanda yake da tsawon daƙiƙa 12 a ranar 5 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Zaben fitar da gwani: An aike da saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu kan gwamnan APC

Alkawarin Tinubu kan rage farashin man fetur
Tinubu bai yi alkawarin rage farashin man fetur ba Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Bidiyon ya nuna wani mutum yana kwaikwayon shugaban ƙasa. Taken da ke cikin bidiyon yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A ƙarshen watan Agusta, za a sayar da man fetur a kan N100 kowace lita - Bola T, 2023."

Yadda aka sauya bidiyon Tinubu

A cikin faifan bidiyon da ke ƙara jan hankula tun lokacin da aka sanya shi, an ji muryar da ke kwaikwayon Tinubu tana cewa:

"Ina so na gaya wa ƴan Najeriya cewa abubuwa suna tafiya daidai kuma za a sayar da mai a kan Naira 100 kan kowace lita a ƙarshen watan Agusta."

Kafin zuwan ranar 10 ga watan Afrilu, mutane sama da 89,000 suka kalli bidiyon, ya samu sharhi kusan 200, mutum sama da 700 suka sake wallafa shi, yayin da mutum sama 100 suka adana shi.

Wasu mutane sun yi ba'a ga sanarwar kuma sun ce ƙarya ce sannan ƙage ce, yayin da wasu ke ganin bidiyon na gaskiya ne.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Ganduje ya bayyana abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi wa Tinubu

Menene gaskiya game da bidiyon?

A cewar Dubawa an gano cewa bidiyon sauya shi aka yi. Leɓɓan Tinubu sun motsa saɓanin abin da fuskarsa ke nunawa.

Akwai bambanci kan maganar da yake yi da abin da leɓɓensa ke nunawa. Sannan an gano an yi amfani da wani abu na gyaran murya a bidiyon wanda ya ƙara tabbatar da na ƙarya ne.

Dandalin binciken ya yi amfani da wani abin bincike na deepware.ai, domin tabbatar da ingancin bidiyon.

Binciken ya nuna cewa bidiyon na ƙarya ne, wanda ke cike da abubuwan zargi.

Matawalle ya goyi bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro ya caccaki masu sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Bello Matawalle ya bayyana cewa duk wanda baya ganin ayyukan alherin da shugaban ƙasan yake yi, to tabbas yana cikin sahun makafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel