Kungiya Ta Ja Kunnen Gwamna Abba Kan Binciken Ganduje, An Ba Shi Shawarar Abin da Ya Kamata Ya Yi

Kungiya Ta Ja Kunnen Gwamna Abba Kan Binciken Ganduje, An Ba Shi Shawarar Abin da Ya Kamata Ya Yi

  • Wata ƙungiya ta yi Allah wadai da yunƙurin da gwamnatin jihar Kano ta yi na binciken tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje
  • Ƙungiyar ta yi nuni da cewa binciken tsohon gwamnan ba shi ba ne abin da ya damu al'ummar jihar a halin yanzu ba
  • Ta buƙaci gwamnan da ya mayar da hankali wajen tsamo al'ummar jihar daga halin da suka samu kansu a ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata ƙungiya a ƙarƙashin ƙungiyar Kano Concerned Forum (KCF) ta yi Allah-wadai da shirin gwamnatin jihar Kano na binciken gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Ƙungiyar ta bayyana cewa dawo da batun binciken gwamnatin Ganduje, alamu ne na cewa gwamnatin yanzu ta yarda da cewa ta kasa taɓuka komai, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya kawo mafita ga yan Najeriya kan ƙoƙarin Tinubu na kawar da ƴan bindiga

An gargadi Gwamna Abba Kabir Yusuf
Binciken Ganduje ya jawo ana sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf, Abdullahi Umar Ganduje - OFR
Asali: Facebook

Sakataren ƙungiyar kwamared Auwal Shu’aib, shi ne wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar, yayin da yake jawabi ga manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnati mai ci ta Abba Kabir Yusuf ta mayar da hankali hankali kan yadda za ta ciyar da jihar gaba, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

A cewarsa:

"An yi zaɓe kuma ya wuce. Yanzu lokaci ya yi da mutanen jihar Kano za su kwashi romon dimokuraɗiyya."

Wace shawara aka ba Gwamna Abba?

Ya ƙara da cewa, idan da a ce gwamnatin Gwamna Abba ta shirya kawo ci gaba, ba za ta ɓata lokacinta mai daraja ba kan batun binciken gwamnatin Ganduje da iyalansa ba.

A kalamansa:

"Kusan shekara guda kenan da gwamnati ta karɓi ragamar mulki, amma ba ta taɓuka komai ba, kuma muna mamakin dalilin da ya sa take ɓata lokaci a kan abin da ba mai samuwa ba ne."

Kara karanta wannan

Watanni 2 da maganar komawa APC, Abba ya dauko binciken Ganduje da iyalinsa

"Mutanen Kano sun fi damuwa da a fitar da su daga cikin ƙangin da suka samu kansu a ciki."
"Saboda haka, wannan kwamitin maras amfani, ba domin komai aka kafa shi ba sai saboda siyasa da ɗaukar fansa da son faranta ran wasu mutane a jihar."

An ja kunnen Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Arewa Renaissance Front (ARF) a Kano ta gargadi Gwamna Abba Kabir kan binciken Abdullahi Umar Ganduje.

Ƙungiyar ta bukaci gwamnan ya dakatar shirin binciken inda ta ce hakan bita da kullin siyasa ne kawai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel