Manyan Labarai A Yau
Wani tsohon ma'aikacin babban bankin Najeriya (CBN), ya bayyana a gaban kotu yadda ya karbowa Godwin Emefiele cin hancin $600,000 lokacin da yake jagorantar bankin.
Darajar Naira ta yi raga-raga a satin da ya gabata da kaso 23%. Masana sun gano cewa wayau da ake nunawa wajen cinikin Dala ya jawo Naira ta fadi a kasuwa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kusa cika shekara daya a kan karagar mulkin Najeriya. Shugaba Tinubu zai yi wa majalisar ministocinsa garambawul.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar yayan tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko. Marigayin ya rasu ne bayan 'yar gajeruwar rashin lafiya.
An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a kan hanyar Okene-Lokoja da ke jihar Kogi. Hatsarin motan ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan mutum 19.
Jam'iyyar All Progressives Peoples Congress (APC), za ta bayar da satifiket din lashe zaben fidda gwanin gwamnan jihar Ondo, ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya shawarci Alhaji Yahaya Bello da ya daina wasan buyan da yake yi, ya fito ya kai kansa ga hukumar EFCC.
Kwamitin binciken shari'a da gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kafa, zai fara zamansa domin binciken gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Kungiyar 'Concerned North-Central APC Stakeholders' ta nesanta kanta daga zanga-zangar neman tsige Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari