Tsohon Ma'aikacin CBN Ya Fallasa Yadda Ya Karbowa Emefiele Cin Hancin Dala 600,000

Tsohon Ma'aikacin CBN Ya Fallasa Yadda Ya Karbowa Emefiele Cin Hancin Dala 600,000

  • Wani tsohon ma’aikacin babban bankin Najeriya (CBN) ya bayar da shaida a shari'ar da ake yi wa tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele
  • Ma’aikacin wanda ya yi aiki a bankin na tsawon shekara takwas, ya shaida wa kotu yadda ya taimakawa Emefiele wajen karɓar cin hancin Dala 600,000
  • Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa wani lokaci na gaba domin tabbatar da ko shaidan tilasta masa aka yi ko kuma yana da hannu a cikin shirin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Wani sabon shaida ya bayyana a shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, inda ya bayar da sababbin bayanai ga kotu.

Shaidan mai suna Mista John Ayoh, wanda tsohon ma'aikaci ne a babban bankin, ya bayar da shaida a gaban kotun laifuka na musamman da ke Ikeja a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Samuel Ortom ya shawarci tsohon gwamnan Kogi kan binciken EFCC

Shaida ya fallasa Emefiele
Tsohon ma'aikacin CBN ya ba da shaida kan Godwin Emefiele a kotu Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

John Ayoh ya bayyana cewa ya shafe shekara takwas yana aiki a babban bankin na Najeriya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CBN: Wa ya gabatar da shaidan a kotu?

Lauyan hukumar ECCC, Mista Rotimi Oyedepo (SAN), ne ya gabatar da shaidan a gaban kotun.

John ya bayyana cewa ya samu kira daga hukumar EFCC kan harkokin kasuwanci guda biyu da ya gudanar ta hannun Emefiele.

Ya bayyana cewa ya karɓi kuɗaɗen na farko, da suka kai Dala 400,000 a cikin ambulan, a gidansa da ke Lekki Phase One, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

John ya kuma bayyana cewa ya karɓi kudaɗen na biyu ne Dala 200,000 a babban ofishin CBN da ke Legas.

"Mutumin da ya kawo kuɗaɗen na biyu ya zo ofishinmu da ke Legas inda na fadawa Emefiele amma sai ya ce baya son ya ga wani saboda haka na kawo ambulan ɗin da kaina."

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya daka tsalle ya fada kogin Legas, 'yan sanda sun magantu

- John Ayoh

Ya bayyana cewa ya bi umurnin Emefiele inda ya kai masa kuɗaɗen da kansa shi kaɗai ba tare da wani ba.

"Tilasta masa aka yi" inji shaida

Shaidan ya bayyana cewa tilasta masa aka yi kuma ya ba da shaidar bayanansa ga mai shari'a Rahman Oshodi.

John Ayoh ya bayyana cewa EFCC ta gayyace shi ne a ranar, 17 ga watan Fabrairu, kuma ba a tsare shi ba inda aka bayar da belinsa.

Bayan ya gabatar da shaidarsa, alƙalin kotun ya ɗage ƙarar har zuwa ranar, 3 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraronta.

An ba da belin Emefiele

A wani labarin kuma, kun ji cewa alƙalin kotun laifuffuka ta musamman da ke Ikeja a jihar Legas, ya bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele a kan N50m.

Tsohon gwamnan na CBN yana fuskantar tuhume-tuhume guda 26 da suka haɗa da karkatar da Dala biliyan 4.5 da kuma Naira biliyan 2.8.

Asali: Legit.ng

Online view pixel