TikTok: Cikakken Jerin Kasashe 25 da Aka Hana Amfani da Manhajar

TikTok: Cikakken Jerin Kasashe 25 da Aka Hana Amfani da Manhajar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kwanan nan Shugaban Amurka, Joe Biden, ya rattaɓa hannu kan wani kudirin wanda zai hana amfani da TikTok a kasar Amurka, idan kamfanin ByteDance na China, bai sayar da shi cikin shekara ɗaya ba.

Ƴan majalisar dokokin Amurka sun damu kan barazanar tsaron ƙasa da ke da alaƙa da manhajar, musamman idan gwamnatin China tana samun bayanan da TikTok ke tattarawa, cewar rahoton jaridar CNN.

Kasashen da aka hana amfani da TikTok
Akwai kasashe akalla 25 da sun hana amfani da TikTok Hoto: SOPA Images
Asali: Getty Images

Ƙasashe da dama sun ɗauki matakin taƙaitawa ko hana amfani da TikTok, inda suke nuna damuwa kan bayanan sirri, tsaro ko batututuwan ɗa'a.

Ƙasashe daban-daban sun bi mabambantan hanyoyi kan hana amfani da TikTok, inda wasu suka hana amfani da shi gabaɗaya, yayin da wasu suka hana amfani da shi a na'urorin gwamnati ko hana amfani da wasu abubuwan da ya ƙunsa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban PDP tare da sace mawaki a Delta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Punch ta jero ƙasashen da suka aiwatar da nau'i daban-daban na haramci a kan TikTok.

Ƙasashe masu hana Tik Tok gaba ɗaya

1. China

Nau'in TikTok na ƙasa da ƙasa ba a amfani da shi a China. A maimakon hakan sai dai mutane su ɗauko Douyin, kishiyar TikTok na China, wanda gwamnatin ƙasar ta sanya matakai masu tsauri a kansa.

2. Sanagal

Sanagal ta hana amfani da TikTok gaba ɗaya bayan zargin cewa wani ɗan takarar adawa yana amfani da manhajar wajen yaɗa saƙonnin ƙiyayya da ɓarna.

3. Somaliya

Gwamnatin Somaliya a hukumance ta haramta amfani da TikTok, Telegram, da 1XBet - wata kafar caca a yanar gizo a watan Agustan 2023.

4. Koriya ta Arewa

An taƙaita samun damar amfani da yanar gizo sosai ga yawancin ƴan ƙasar Koriya ta Arewa. Yayin da ake bari a yi amfani da wasu tsirarun manhajoji a ƙasar, TikTok ba shi daga cikin waɗanda ake amfani da su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari a wasu kauyukan Neja bayan sojoji sun janye

5. Afghanistan

A watan Afirilun 2022, gwamnatin Taliban ta ɗauki matakin hana amfani da TikTok, inda ta nuna damuwa kan rawar da yake takawa a kan matasa.

6. Indiya

Indiya ta hana amfani da TikTok a shekarar 2020 bayan wani rikici kan iyakoki tsakanin China da Indiya a shekarar 2020.

7. Iran

TikTok da sauran manhajoji da suka yi suna a duniya kamar irinsu X da Facebook duk an hana amfani da su a Iran.

8. Uzbekistan

Tun daga watan Yulin 2021, an hana amfani da TikTok a Uzbekistan saboda iƙirarin da hukumomi suka yi na cewa manhajar ba ta bin ƙa'idojin kare bayanan mutane na ƙasar.

Ƙasashe masu hani bana gaba ɗaya ba

1. Indonesia

2. Kyrgyzstan

3. Rasha

Ƙasashe masu hani a na'urorin gwamnati

1. Canada

2. Australiya

3. Austria

4. Denmark

5. Estonia

6. Tarayyar Turai (EU)

7. Faransa

8. Amurka

9. UK

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Lauya ya hango kuskuren hukumar EFCC, ya yi gargadi

10. Ireland

11. Malta

12. Latvia

13. Taiwan

14. Belgium

Sana'o'in koyo a shekarar 2024

A wani labarin kuma, kun ji cewa akwai manyan fasahohi da mutum zai koya a yanar gizo waɗanda ake neman masu ƙwarewa kan su a faɗin duniya.

Fasahohin bincike da sarrafa bayanai da ilmin ƙirƙirar manhajoji na daga cikom sana'o'in da ake samun kuɗade masu kyau da su yanzu a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel