Tsadar Rayuwa: Akpabio Ya Ba 'Yan Najeriya Hakuri, Ya Fadi Babban Mai Laifi Kan Halin da Ake Ciki

Tsadar Rayuwa: Akpabio Ya Ba 'Yan Najeriya Hakuri, Ya Fadi Babban Mai Laifi Kan Halin da Ake Ciki

  • Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya buƙavi ƴan Najeriya da su ƙara yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu haƙuri
  • Akpabio ya bayyana cewa shugaban ƙasan na bakin ƙoƙarin wajen gyara ɓarnar da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya yi
  • Ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa Shugaba Tinubu zai dawo da tattalin arziƙin bisa kan turba saboda ƙwarewar da yake da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Akwa Ibom - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Akpabio ya bayyana cewa Tinubu yana ƙoƙarin gyara tattalin arziƙin ƙasar nan ne wanda ya zargi tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, da yi masa babban giɓi.

Kara karanta wannan

Binciken Matawalle: An yi sabuwar fallasa kan masu zanga-zanga a EFCC

Akpabio ya ba 'yan Najeriya hakuri
Akpabio ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri da Shugaba Tinubu Hoto: @DOlusegun, @GodwinIEmefiele
Asali: Twitter

Tattalin arziƙi ya taɓarɓare

Akpabio ya yi nuni da cewa Shugaba Tinubu ya gaji tattalin arziƙi ne wanda ya kusa durƙushewa inda yanzu yake ƙoƙarin yin amfani da basirarsa wajen ceto shi, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar dattawan ya yi wannan roƙon ne a filin wasa na Ikot Ekpene da ke jihar Akwa Ibom a ƙarshen mako a wajen wata liyafa da aka shirya masa tun bayan zamansa shugaban majalisar.

Ya bayyana cewa yana kan bakansa na cewa Emefiele ne babban mai laifi kan halin da tattalin arziƙin ƙasar nan yake ciki duk kuwa da ƙarar da tsohon gwamnan na CBN ya kai shi kotu saboda cewa hakan.

Tinubu zai gyara tatttalin arziƙi

Ya nuna ƙwarin gwiwarsa cewa Tinubu zai dawo da tattalin arziƙin ƙasar nan kan turba kamar yadda ya yi a jihar Legas lokacin da ya riƙe muƙamin gwamna

Kara karanta wannan

Matawalle: EFCC ta yi magana kan binciken tsohon gwamnan Zamfara

Ya haƙiƙance cewa tsofaffin gwamnoni uku da ke da muƙami mafi girma a ƙasar nan, ilmin da suke da shi da ƙwarewarsu zai sanya su ceto ƙasar nan.

Ya ce ƙwarewar Tinubu tsohon gwamnan Legas a matsayin shugaban ƙasa, Kashim Shettima tsohon gwamnan Borno a matsayin mataimakin shugaban ƙasa da shi kansa a matsayin tsohon gwamnan Akwa Ibom, za ta sanya su dawo da ƙasar nan kan turbar ci gaba.

An buƙaci Akpabio ya yi murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar PDP ta buƙaci Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta sauka daga kan kujerarsa ta shugaban majalisar dattawa.

PDP ta ce hakan ne kawai zai ba da damar a gudanar da bincike kan zargin cewa an yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kudin 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel