Fubara vs Wike: Gwamnan PDP Ya Fadi Makomar Rikicinsa da Ministan Tinubu

Fubara vs Wike: Gwamnan PDP Ya Fadi Makomar Rikicinsa da Ministan Tinubu

  • Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya bayyana darussan da ya koya sakamakon matsin lambar da ya shiga saboda rikicin siyasar jihar
  • Gwamnan ya bayyana cewa matsin lambar ya sanya ya ƙara mayar da hankali domin ganin ya samu nasara wajen sauke nauyin da ke kansa
  • Ya bayyana cewa a wajensa da mutanen jihar, rikicin ya zo ƙarshe yanzu lokaci ne na gudanar da shugabanci mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya bayyana cewa rikicin siyasar da aka yi fama da shi a jihar ya zo ƙarshe.

Gwamnan ya bayyana cewa hakan ya sanya gwamnatinsa ta mayar da hankali waje samar da shugabanci mai kyau a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shirya daukar mataki mai tsauri kan dan kwangila saboda aikin N6bn

Fubara ya magantu kan rikicin Ribas
Gwamna Fubara ya ce rikicin siyasar Ribas ya zo karshe Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi bakuncin mambobin kwamitin majalisar wakilai kan ƙararrakin jama’a, ƙarƙashin jagorancin, Hon. Mike Etaba, a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal, a daren ranar Asabar, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana cewa a wajensa da sauran mutanen jihar Ribas, babu wani rikicin siyasa da ya yi saura a yanzu, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Me Fubara ya ce kan rikicin siyasar jihar?

Da yake bayar da misali da wani fim da ya kalla a baya, gwamnan ya yi bayanin yadda matsin lambar rikicin ta sanya ya ƙare zage damtse domin gudanar da shugabanci.

"Mu a wajenmu babu wani rikicin siyasa. Na kalli wani fim shekarun baya mai suna ‘Devil’s Advocate.’ Na yi amanna cewa wasu daga cikinku su ma sun kalli fim ɗin.

Kara karanta wannan

UTME 2024: Gwamnan Kwara ya mika sako ga daliban da suka ci mai yawa a JAMB

"Ɗaya daga cikin taurarin fim ɗin, Al Pacino, ya ce matsin lamba na sa wasu su ja da baya ko su gaza, wasu kuma yana sanyawa su mayar da hankali domin yin nasara. Mun zaɓi mu mayar da hankali a cikin wannan matsin lambar.
"Shi ya sa muke ci gaba. Shi ya sa muke yin tasiri mai kyau a rayuwar mutanenmu. Mulki ya shafi mutane ne, ba batun ka yi wa kanka bane."
"Mulki abu ne na biyan muhimman buƙatun mutanen da muke jagoranta, kuma da yardar Allah na musamman, muna yin hakan."

- Siminalayi Fubara

Gwamna Fubara ya sha alwashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara, na jihar Ribas ya sha alwashin cewa ba zai mulki jihar ta hanyar durƙusawa wani ba.

Gwamnan wanda yake taƙun saka da magabacinsa Nyesom Wike, ya buƙaci ƴan asalin jihar su mara masa baya ya ceto ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel