Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da barkewar cutar Kyanda a wasu kananan hukumomim jihar. Cutar wacce ta kama mutane da dama ta yi sanadiyyar rasuwar mutum 42.
Gwamnatin jihar Sokoto ta shirya sayo babura da keke Napep domin samarwa da matasa ayyukan yi. Majalisar zartaswar jihar ta amince da hakan a yayin taron ta.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kare matakin gwamnonin Arewa na zuwa kasar Amurka taro kan matsalar rashin tsaron da ta addabi yankin.
Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta yi magana kan binciken tsohom gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, kan zargin karkatar da N70bn.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta sanar da adadin 'yan ta'addan da sojoji suka hallaka a cikin watan Afirilu tare da adadin mutanen da aka ceto wadanda aka sace.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi wa jami'an 'yan sa-kai na CJTF kwanton bauna a jihar Sokoto. Miyagun sun hallaka jami'ai tara tare da raunata wasu da dama.
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa ta kammala binciken kan harin bam wanda ya hallaka masu gudanar da Mauludi a kauyen Tudun Biri na jihar Kaduna.
Wasu daga cikin gwamnonin Najeriya, sun yi wa ma'aikatan gwamnati a jihohinsu karin albashi, saboda tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar nan.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar yin galaba kan 'yan ta'adda a jihohin Katsina da Plateau. Sojojin sun sheke dan ta'adda tare da ceto mutum biyu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari