'Yan Bindiga Sun Hallaka Babban Basarake a Wani Hari Cikin Gidansa

'Yan Bindiga Sun Hallaka Babban Basarake a Wani Hari Cikin Gidansa

  • An shiga jimami a ƙauyen Umuihe na yankin Akaeze a ƙaramar hukumar Ivo ta jihar Ebonyi bayan ƴan bindiga sun tafka ta'asa cikin dare
  • Miyagun ɗauke da makamai sun hallaka basaraken ƙauyen, Umazi Ibo Ubani, bayan sun dirar masa har cikin gidansa a daren ranar Juma'a
  • An bayyana rasuwar basaraken a matsayin babban rashi ga mutanen ƙauyen, ƙaramar hukumar da jihar baki ɗaya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ebonyi - Ƴan bindiga sun hallaka Umazi Ibo Ubani, basaraken ƙauyen Umuihe na yankin Akaeze a ƙaramar hukumar Ivo ta jihar Ebonyi.

Kisan basaraken ya jefa mutanen ƙauyen cikin tashin hankali da jimamin wannan babban rashin da suka yi.

'Yan bindiga sun hallaka basarake a Ebonyi
'Yan bindiga sun kashe basarake a Ebonyi Hoto: Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru
Asali: Facebook

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka Dagaci a wani yanayi mara dadi a Kaduna

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa an yi harbe-harbe a ƙauyen bayan da ƴan bindiga suka dira a ranar Juma'a, wanda hakan ya sa mutane suka shiga firgici.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagoran cibiyar yankin Akaeze, Chinasa Okorie ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi da yamma inda ya ce harin ya auku ne da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Juma'a.

Chinasa Okorie ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa basaraken, inda ya jaddada cewa da wuya a samu wani basarake mai irin halayensa, rahoton Daily Post ya tabbatar.

An yi jimamin rashin basaraken

A cewarsa basaraken wanda ya haura shekara 60, jajirtacce ne, mai gaskiya, mai hazaƙa wanda ba shi da tsoro, inda ya ƙara da cewa za a yi kewar ƙwarewar da yake da ita a ƙauyen da ma jihar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Matawalle: EFCC ta yi magana kan binciken tsohon gwamnan Zamfara

A kalamansa:

"Da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Juma'a an kirani a waya cewa an yi harbe-harbe a gidan basaraken mu Umazi Ibo Ubani."
"Bayan an gama harbe-harben mun gano cewa an hallaka basaraken mu na ƙauyen Umuihe a yankin Akaeze na ƙaramar hukumar Ivo."
"Wannan babban rashi ne ga ƙauyen da yankin Akaeze saboda mutum ne mai gaskiya, wanda zai yi wuya a maye gurbinsa saboda yana da hazaƙa sannan ba shi da tsoro."

Ƴan bindiga sun hallaka jami'an CJTF

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun hallaka jami’an ƴan sa-kai na CJTF guda tara a wani mummunan hari a jihar Sokoto.

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan sa-kan ne a wani harin kwanton ɓauna da suka kai musu wanda ya kuma yi sanadiyyar raunata jami'an da ba a tantance adadinsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng