Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Kwara ta ce akalla almajirai 158 ne gwamnatin jihar Kwara ta kwashe daga titunan Ilorin tare da mayar da su jihohinsu a cikin shekara daya.
Shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin sama. Ya zama shugaban kasa na 15 da ya rasu sakamakon hatsarin jirgin sama.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daliban da kawai ke karatu a makarantun gwamnatin tarayya ne za su amfana da shirin ba dalibai rancen kudin karatu.
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta yi fatali da bukatar da Tukur Mamu ya gabatar a gabanta kan mayar da shi gidan yarin Kuje.
Shugaban juyin juya hali na kasar Iran, Ayatullah Ali Khamenei ya sanar da cewa za a yi kwanaki biyar ana zaman makokin shugaban kasar, Ebrahim Raisi da ya rasu.
Ministar masana'antu ciniki da juba jari, Doris Anite za ta halarci taron zuba jari na 'yan Najeriya mazauna kasashen waje tare da Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar rage mugun iri bayan ta hallaka 'yan bindigan da suka addabi jama'a. An kuma kwato makamai a hannunsu.
An tabbatar da rasuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi da wasu jami'an gwamnatin kasar a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya ritsa da su.
Kotun Burtaniya ta ɗaure mutumin da aka kama da laifin kisan matarsa, ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari har ƙarshen rayuwarsa bayan kama shi da laifin kisa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari