Dakarun Sojoji Sun Sheke 'Yan Ta'adda 7, Sun Kwato Makamai Masu Yawa a Kaduna

Dakarun Sojoji Sun Sheke 'Yan Ta'adda 7, Sun Kwato Makamai Masu Yawa a Kaduna

  • Dakarun sojojin Najeriya da ke aikin samar da tsaro a jihar Kaduna sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda a yayin arangamar da suka yi a jihar
  • Sojojin sun hallaka ƴan ta'adda bakwai a ƙaramar hukumar Chikun bayan sun fita wani aikin sintiri domin kakkaɓe miyagu a ranar Lahadi
  • Jami'an tsaron sun kuma ƙwato tarin makamai daga hannun ƴan ta'addan waɗanda suka daɗe suna addabar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun runduna ta ɗaya ta sojojin Najeriya da ke aiki a Kaduna sun kashe ƴan ta'adda bakwai a ƙauyen Udawa da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar.

Dakarun sojojin sun samu wannan nasarar ne a wani aikin sintiri da suka gudanar a kan hanyar Udawa-Kurebe a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga yanayi yayin da ƴan bindiga suka kashe sojojin Najeriya

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Kaduna Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da muƙaddashin daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Laftanal Kanal Musa Yahaya ya fitar, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka sheƙe ƴan ta'adda

A yayin sintirin sojojin sun yi arangama da ƴan ta'adda inda suka samu nasarar hallaka guda biyar daga cikinsu, rahoton da jaridar Leadership ya tabbatar.

Sojojin sun kuma ƙwato makamai da dama daga hannun ƴan ta’addan da suka haɗa da wata jigida ta bindigar AK-47 da babu komai a ciki, babbar bindiga ɗaya, harsashi shida da sauran makamai masu hatsari.

Hakazalika, sojojin rundunar a wani samame da suka kai a ƙauyen Kwaga da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda biyu.

Sojojin sun kuma ƙwato bindigogi guda biyu ƙirar AK-47, jigida guda biyu da babura guda biyu daga hannun ƴan ta'addan.

Kara karanta wannan

'Mutuwar' wani matashi Kabiru sakamakon azabtarwar ƴan sanda ya tada ƙura a Najeriya

Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar sojojin Najeriya sun kashe ɗan bindiga ɗaya yayin da suke hanyar zuwa kai hari a titin Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Tawagar miyagun ƴan bindigar sun fito da nufin zuwa kai hari, kwatsam sojoji suka masu kwantan ɓauna suka hallaka ɗan bindiga ɗaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel