Manyan Labarai A Yau
Kima da darajar Naira yana faduwa war-wasa a makon nan. Akwai karancin daloli a kasuwannin bayan fage da bankuna, wannan ya tilasta faduwar kimar Naira a Najeriya.
Sanata mai wakiltar Borno ta Tsakiya a majalisar dattawa ya caccaki matakin da gwamnatin tarayya ta hannun bankin CBN ya dauko na kawo harajin yanar gizo.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda masu tarin yawa a cikin mako guda a fadin kasar nan. Sojojin sun kuma ceto mutanen da aka sace.
An samu asarar rayukan mutum hudu bayan wata bakuwar cuta barke a jihar Zamfara. Cutar ta kama mutane da dama yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya bayyana a gaban kotu kan zargin badaƙalar N7.2bn. Sirika ya yi magana kan yiwuwar tafiya gidan kurkuku.
Dubunnan mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Jigawa sun watsar da jam'iyyar inda suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta NNPP.
Fadar shugaban kasa ta saki bidiyon Bola Ahmed Tinubu yana tafiya zuwa ofis dinsa tun bayan dawowarsa gida Najeriya daga ziyarar da ya kai kasashen waje.
Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya ziyarci majalisar dokokin jihar Rivers yayin da ake batun 'yan majalisar sun fara yunkurin tsige shi daga kan kujerarsa.
Kungiyar matasan Arewa ta NEYGA ta bukaci Sanata Ali Ndume ya msyar da hankali kan abin da ya kai shi majalisa ba ya tsaya yana wasu kananan kalamai ba.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari