Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta nuna rashin amincewa da hukuncin kotu wanda ya sanya mata tarar N10m kan Aminu Ado Bayero.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karrama wasu daga cikin jami'an tsaro na rundunar Askarawan Zamfara kan kwazon da suka nuna wajen yakar 'yan bindiga.
Dubunnan mata suna mutuwa a duk shekara musamman bayan samun juna biyu ko haihuwa. Dr. Zainab Mahmud likita ce a Amurka da ke da burin kawo gyara a Najeriya.
A yayin da ake shirin yin babbar Sallah a Najeriya, darajar Naira ta fadi kasa warwas a kasuwannin yan canji. Naira ta yi kasa kan Dalar Amurka a kasuwa.
Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya taya gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, murnar zuwan babbar Sallah.
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan yiwuwar sake rasa sarautar gidan Dabo a nan gaba. Sarkin ya nuna cewa komai nufin ubangiji ne.
Hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS) ta bukaci al'ummar musulmi da su yi taka tsantsan yayin gudanar da ibadah da bukukuwan babbar Sallah da ke tafe.
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Whirl Punch, sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda guda shida yayin wani artabu da suka yi a jihar Kaduna.
Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ola Olukoyode, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu bai yiwa hukumar katsalandan.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari