Likita Ta Bayyana Abin da Yake Kashe Dubunnan Mata a Boye Duk Shekara a Najeriya

Likita Ta Bayyana Abin da Yake Kashe Dubunnan Mata a Boye Duk Shekara a Najeriya

  • Dr. Zainab Mahmoud likita ce daga Arewacin Najeriya wanda ta samu kwarewa kuma ta ke aiki a kasar Amurka
  • Babbar likitar ta zama gwana wajen cututtukan zuciya musamman idan larurar ta shafi mata masu juna biyu
  • Wasu suna tserewa kasashen ketare, amma burin Dr. Zainab Mahmoud shi ne ta dawo mahaifarta Najeriya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

America - Dr. Zainab Mahmoud kwararriyar likita ce wanda ta tashi a Kano, amma yanzu ana alfahari da ita a asibitocin kasar waje.

Dr. Zainab Mahmoud ta kware ne a harkar ilmin cututtukan zuciya musamman abin da ya shafi ciwon a jikin mata masu juna biyu.

Dr. Zainab Mahmoud
Dr. Zainab Mahmoud likita ce da ta ciri tuta a Amurka Hoto: @iNabmahmoud, internalmedicine.wustl.edu
Asali: UGC

Hira da likitar zuciya, Dr. Zainab Mahmoud

A wata hira da aka yi da ita a shirin ‘Idan ka ji wane ba banza ba’ a dandalin Facebook, Dr. Zainab Mahmoud ta fadi inda ta sa gaba.

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Likitar tana da difloma a harkar cututtuka a wata jami’a da ke Landan da kuma digirgir a annin tsare-tsaren lafiya a Imperial College.

Yanzu haka ta na aiki a sashen cututtukan zuciya a asibitin jami’ar Pennsylvania a Amurka kuma ta sha alwashin dawowa gida Najeriya.

Illar cutar hawan jini a Najeriya

Rahotannin Premium Times da wasu jaridu sun nuna ana rasa mata 40, 000 zuwa 80, 000 wajen haihuwa duk shekara a jihohin Najeriya.

Hawan jini yana cikin abin da ya fi illa, ana rasa mutum fiye da 200, 000 a kasar nan.

Daga cikin abubuwan da ke jawo mace-macen mata akwai cutar zuciya da makamantansu kuma Najeriya ce ta daya a duniya.

Likitar ta ce burinta a kawo gyara a kasarta musaman Arewacin Najeriya da jihar Kano, a rage rasa rayukar mata ga cutar hawan jini.

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Za a fassara huɗubar Arafah zuwa Hausa da wasu harsuna 19 na duniya

Likita ta fadi matsalar cutar hawan jini

Daga cikin inda ake samun matsaloli shi ne rashin ba da magani wanda samun magani yake rage hawan jini sosai wajen masu juna biyu.

A cewarta, bincike ya nuna akalla 75% na mutane ba su samun maganin hawan jini duk da cewa magungunan ba su da tsada a asibitoci.

An dade ana amfani da magungunan, amma kuma jahilci ya hana matan Najeriya sanin illar da cutar zuciya za ta yiwa mai ciki.

Mata da yawa ba su san hawan jini yana kisa ba musamman a kananan shekarun rayuwa.

Likita tana so a kawo gyara a asibiti

Wata hanya da ta ke ganin za ta bi domin a kawo gyara shi ne hada kai da sauran likitoci kananan asibitoci wajen canza masu dabi’a.

Baya ga karfafa sauran likitoci, ta na so malaman asibiti su zama masu dadin mu’amala da marasa lafiya, su daina nuna kaushin hali.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da babban malamin addini a Kaduna, rundunar 'yan sanda ta magantu

Hadiza Galadanci: Likita mai ceto masu ciki

Ku na da labari cewa duk da Hadiza Shehu Galadanci ta zama Farfesa kuma babbar likita a duniya, ba ta manta da kula da iyalinta ba.

Farfesar da tayi fice a duk fadin duniya ta ce idan ta dawo daga asibiti, abin da yake gabanta shi ne tarbiyyar gidanta da makamantansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng