Gwamnatin Abba Ta Bayyana Matsayarta Kan Tarar N10m da Aka Sanya Mata Kan Aminu Ado

Gwamnatin Abba Ta Bayyana Matsayarta Kan Tarar N10m da Aka Sanya Mata Kan Aminu Ado

  • Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf tmba ta gamsu da tarar N10m da kotu ta sanya mata ba kan shari'ar Aminu Ado Bayero
  • Kwamishinan shari'a na jihar ya bayyana cewa lauyoyin gwamnati na duba hukuncin kotun da nufin ɗaukaka ƙara a kai
  • Kwamishinan ya kuma koka kan yadda ƴan sanda ke karɓar umarni daga sama duk da cewa Gwamna Abba shi ne babban jami'in tsaro a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ƙi amincewa da cin tarar Naira miliyan 10 da kotu ta umarci ta biya saboda take haƙƙin ɗan Adam na Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

A ranar Juma’a ne wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta sanya tarar a kan gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, babbar kotu ta yanke hukunci a shari'ar sarautar Kano

Gwamnatin Abba ta ki amincewa da tarar N10m kan Aminu Ado Bayero
Gwamnatin Kano ta ki amincewa da tarar N10m da kotu ta sanya mata kan Aminu Ado Bayero Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Matsayar gwamnatin Abba kan tarar N10m

Sai dai a yayin wata ganawa da manema labarai a gidan gwamnati inda gwamnan ya samu wakilcin Antoni Janar na jihar kuma kwamishinan shari’a, Haruna Dederi, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haruna Dedieri ya ɗora alhakin abin da ke faruwa a jihar a kan wasu maƙiyan jihar waɗanda suke son ganin sun kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Gwamnati ba ta tauye haƙƙin Aminu Ado Bayero ba

Kwamishinan ya musanta cewa gwamnatin jihar ta tauye haƙƙin ɗan Adam na Aminu Ado Bayero, wanda ta sauke daga kan sarauta, inda ya ƙara cewa lauyoyin gwamnati na duba hukuncin da nufin ɗaukaka ƙara a kai.

Haruna Dederi ya kuma koka kan yadda ƴan sanda ke ci gaba da karɓar umarni daga sama duk da cewa gwamnan shi ne babban jami’in tsaro na jihar.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: Babbar kotu za ta yanke hukunci a shari'ar sarautar Kano

Ya ƙara da yin kira ga ƴan Najeriya masu kishin ƙasa da abokan arziki daga ƙasashen duniya da su shiga tsakani domin a samu zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a jihar.

Aminu Ado Bayero ya aika da sako ga Abba da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya taya shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, murnar bukukuwan Sallah.

Sarkin ya kuma sanar da cewa an dakatar da gudanar da hawa da aka shirya tun da farko biyo bayan shawarwarin da jami’an tsaro suka bayar domin a ci gaba da samun zaman lafiya a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng