Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Yayin Artabu a Jihar Kaduna

Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Yayin Artabu a Jihar Kaduna

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri na ƴan ta'addan da suka addabi mutane a jihar Kaduna
  • Sojojin na rundunar Operation Whirl Punch sun yi nasarar sheƙe ƴan ta'adda mutum shida a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar wanda ya bayyana hakan ya kuma ce sojojin sin ƙwato makamai a hannun ƴan ta'addan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun sojoji na rundunar Operation Whirl Punch da bataliya ta musamman ta 198 ta sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda shida a jihar Kaduna.

Dakarun sojojin sun kashe ƴan ta'addan ne a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka rikakken shugaban 'yan bindiga da mayakansa 35 a Arewa

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Kaduna
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda shida a Kaduna Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojojin sun gudanar da wani samame na musamman a Birnin Gwari bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ƴan ta'adda a yankin, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka hallaka ƴan ta'adda

Kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar

Samuel Aruwan ya ce sojojin sun fara aikin ne da samun nasarar kawar da maɓoyar ƴan ta'adda a ƙauyukan Maidaro, Ngade Alha, Dogon Dawa, Damari, Saulawa, Farin Ruwa, Maganda, Sabon Layi da Kampanin Doka.

"Da isar su Saulawa, sun yi musayar wuta da ƴan ta'adda inda suka hallaka mutum biyu. Sun kuma ƙwato babur guda ɗaya da rediyo guda ɗaya."
"Dakarun sojojin sun sake yin musayar wuta da ƴan ta'adda a Farin Ruwa, inda suka hallaka abokan gaba mutum huɗu."

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun mayar da martani, sun halaka ƴan bindiga da yawa a Arewa

"Dakarun sojojin sun share yankin inda suka ƙwato GPMG guda ɗaya, bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, jigida guda shida na AK-47, bindiga ƙirar FN, harsasai guda 22 na NATO masu kaurin 7.62mm."
"Sauran sun haɗa da harsasai na musamman masu kaurin 7.62mm guda 55 da babur guda ɗaya."

- Samuel Aruwan

Sojoji sun hallaka ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na Operation Whirl Punch sun kashe ƴan bindiga biyar a yankin Dantarau na ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Dakarun sojojin sun je wani aikin sintiri ne a yankin Kachia-Kajuru a lokacin da suka ci karo da ƴan bindigan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng