Dangote Ya Ziyarci Tinubu Bayan An Sauko Sallah, Hotuna Sun Bayyana

Dangote Ya Ziyarci Tinubu Bayan An Sauko Sallah, Hotuna Sun Bayyana

  • A ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote
  • Aliko Dangote ya je gaisuwar Sallah ga shugaban ƙasa Tinubu domin bikin babbar Sallah a gidansa da ke Ikoyi a jihar Legas
  • Ƴan Najeriya sun mayar da martani kan gaisuwar Sallah da Dangote ya je yiwa Shugaba Tinubu bayan an kammala Sallar Idi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ikoyi, jihar Legas - Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya je gaisuwar Sallah wajen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas.

Shugaba Tinubu dai yaje jihar Legas ne domin gudanar da hutun babbar Sallah tare da ƴan uwa da abokan arziƙi.

Kara karanta wannan

Bayan tsige Mamman Ahmadu, Tinubu ya ba tsohon kwamishinan Legas wani babban muƙami

Dangote ya ziyarci Tinubu
Dangote ya je gaisuwar Sallah wajen Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Dangote ya ziyarci Bola Tinubu

An ɗauki hoton attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika tare da Shugaba Tinubu a gidansa bayan kammala Sallar Idi a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Tinuba kan harkokin sadarwar zamani, Olusegun Dada, ne ya bayyana hakan tare da sanya hoton a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter) @DOlusegun.

Tinubu tare da sauran Musulmi sun yi Sallar Idi a filin Sallar Idi na Dodan Barrack da ke Obalende, Legas a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni.

Wane martani ƴan Najeriya suka yi?

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin da ƴan Najeriya suka yi kan gaisuwar Sallah da Dangote ya je yiwa Tinubu.

@Uchenna94990102 ya rubuta

"Kullum yana neman dalilai ko damar da zai sanya ya ziyarci Tinubu."

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya nemi muhimmiyar bukata wajen 'yan Najeriya kan Bola Tinubu

@kel_chux147 ya rubuta:

"Dangote duk wata gwamnati ce da ke mulki.... ziyarar ba ta kawo wani sauyi ba..."

@sexyyRed002 ta rubuta:

"Mutumin yanzu ya koma binsa domin ya tsira."

@NPaschals ya rubuta:

"Yana neman goyon bayan gwamnati."

@ayoola1952 ya rubuta:

"To sai me? Hakan ya rage farashin garri ko shinkafa?

An buƙaci a yiwa Tinubu addu'a

A wani labarin kuma, kun ji cewa an buƙaci ƴan Najeriya da su sanya shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu cikin addu'a domin ya sauke nauyin da ke kansa.

Sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya yi wannan roƙon inda ya nuna muhimmancin da ke akwai na gwamnatin Tinubu ta yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng