Manyan Labarai A Yau
Wasu miyagun 'yan bindiga sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja inda suka yi awon gaba da fasinjoji masu yawa. 'Yan bindigan sun yi ta'asar ne a cikin dare.
Ranar 12 ga watan Yuni ta koma ranar dimokuradiyya a Najeriya shekarar 2018. Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yi wannan sauyin a lokacin.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta sake neman ciyo bashin Dala 2.5bn daga bankin duniya ne domin aiwatar da wasu muhimman ayyukan da za su amfani kasar nan.
Wata daliba mai karatu a jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutse (FUD) ta kashe jaririyar da ta haifa. Dalibar ta yi wannan aika-aikar nan ta hanyar jefo daga bene.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya dade yana bukatar a yi masa garambawul domin dawo da shi kan turbar da ta dace.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta caccaki kamun ludayin mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya dora alhakin halin kuncin da ake ciki a Najeriya kan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Al'ummar Musulmai za su samu hutu akalla sau biyu a cikin watannin Yuni/Yuli na shekarar 2024. Musulmai za su yi hutun babbar Sallah a cikin watan Yuni 2024.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi nuni da cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai samun cikakkun bayanai kan halin da ake cikin dangane da matsalar tsaro.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari