Ana Cikin Bikin Sallah, Shugaba Tinubu Ya Shilla Zuwa Kasar Waje

Ana Cikin Bikin Sallah, Shugaba Tinubu Ya Shilla Zuwa Kasar Waje

  • Shugaban ƙasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bar ƙasa domin zuwa birnin Pretoria na ƙasar Afirika ta Kudu a ranar Talata, 18 ga watan Yunin 2024
  • Shugaba Tinubu ya shilla zuwa birnin ne domin halartar bikin rantsar da shugaban ƙasar, Cyril Ramaphosa, bayan ya yi nasarar sake lashe zaɓe
  • Tinubu wanda ya bar Najeriya da misalin ƙarfe 11:06 na safe zai dawo gida ne bayan an kammala bikin rantsar da shugaban na Afirika ta Kudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shilla zuwa birnin Pretoria na ƙasar Afirika ta Kudu.

Shugaban ƙasan ya bar birnin Legas ne da misalin ƙarfe 11:06 na safe a ranar Talata, 18 ga watan Yuni domin zuwa ƙasar ta Afirika ta Kudu.

Kara karanta wannan

Ana shagalin Sallah, Bola Tinubu ya fara samun goyon bayan sake neman takara a 2027

Tinubu ya tafi Afirika ta Kudu
Tinubu ya tafi halartar rantsar da shugaban kasan Afirika ta Kudu Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Meyasa Tinubu ya tafi Afirika ta Kudu?

Shugaba Tinubu ya shilla zuwa ƙasar ne domin halartar bikin rantsar da shugaban ƙasar Afirika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, bayan ya samu nasarar sake lashe zaɓe, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasan ya samu rakiyar gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da saura manyan mutane zuwa filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke birnin Legas, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

An shilla da Shugaba Tinubu zuwa birnin Pretoria na ƙasar Afirika ta Kudu ne a cikin jirgin Dassault Falcon 8X mai lamba 9H-GRC.

Yaushe Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya?

Shugaban ƙasan zai dawo gida Najeriya bayan an kammala bikin rantsar da shugaban ƙasan na Afirika ta Kudu.

Tinubu dai ya je birnin Legas a ranar Juma'a domin hutu da bukukuwan babbar Sallah na wannan shekarar.

A yayin da yake a birnin Legas, shugaban ƙasan ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da yin sadaukarwa wacce za ta sanya ƙasar nan ta samu ci gaba.

Kara karanta wannan

Sallah: Sarkin Musulmi ya yi muhimmiyar tunatarwa ga shugabanni

Tinubu ya yi sabon naɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Ayodeji Gbeleyi a matsayin Darakta-Janar na hukumar kamfanonin gwamnati (BPE).

A yayin sanar da naɗin nasa, Shugaba Tinubu ya nemi sabon shugaban hukumar ta BPE da ya yi amfani ɗumbin ƙwarewar da yake da ita wajen gudanar da wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng