Jihar Legas
Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi karin kudi kan yadda yake sayar da litar fetur. Karin farashin fetur ya fara aiki ne daga ranar daga ranar Litinin.
Fadar shugaban kasa ta musa cewa Bola Tinubu na da dabi'ar sauya mataimaka saboda ya yi aiki da mataimaka 3 a gwamnan Legas. An ce ba za a sauya Shettima ba.
Manyan dilolin mai, Ardova Plc da MRS Oil Nigeria Plc, waɗanda dukkansu abokan huldar matatar Dangote ne, sun rage farashin fetur zuwa N865 a gidaje man su.
Kotun daukaka ƙara mai zama a jihar Legas ta soke hukuncin babbar kotun tarayya na kwace kadarori da wasu maƙudan kudi da ake zargin suna da alaƙa da Emefiele.
Farfesa Wole Soyinka ya bukaci Bola Tinubu ya kaddamar da bincike kan kisan Kudirat Abiola, Bola Ige da Dele Giwa duk da karrama su da ya yi da lambar yabo.
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta sake yin babban rashi bayan rasuwar shugaban karamar hukumar Otto-Awori, Musbau Ashafa ya riga mu gidan gaskiya.
Yayin da ake ranar dimukraɗiyya a kowace ranar 12 ga watan Yuni, dan marigayi MKO Abiola ya bayyana yadda Janar Ibrahim Babangida ya roke su gafara.
Shugabam kasa, Bola Tinubu ya ba marigayi Kudirat Abiola da Janar Shehu Musa Yar’Adua lambar yabo saboda kare dimokuraɗiyya da suka yi a lokacinsu.
Kotun tarayya ta gurfanar da wasu mutane 13 ciki har da dan Indiya bisa zagin sace man disil na Naira biliyan 4 wa Aliko Dangote. An daga shari'ar zuwa Yuli.
Jihar Legas
Samu kari