Labarin Sojojin Najeriya
Wasu kwamandojin 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun mika wuya a hanjun dakarun sojoji a jihar Borno. Sun kuma mika makaman da suke ta'addanci da su.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi maraba da ceto daliban da aka sace a jihar Kaduna da jami'an tsaro suka yi. An ceto daliban ne bayan sun yi kwanaki a tsare.
Hedikwatar tsaro ta kasa ta fitar da bayanai kan daliban da aka ceto daga hannun 'yan bindiga a jihar Kaduna. An dai ceto daliban ne a jihar Zamfara.
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun yi nasarar kashe wani ɗan bindiga mai haɗari da ke sajewa a a matsayin ɗan sanda a jihar Sakkwato.
Wani soja dan asalin jihar Delta mai suna Egitanghan G ya sha alwashin cewa za su dauki fansa kan kisan sojoji 17 da wasu bata gari suka yi a jihar Delta.
Wani matashi ya yi bidiyo inda ya fadi dalilin da ya sa aka kashe sojoji a kauyen Okuama na jihar Delta. Matashin ya ce ba wanzar da zaman lafiya suka je ba.
Dakarun sojoji sun samu nasarar sheke 'yan ta'adda mutum biyu tare da ceto mutum hudu da suka yi garkuwa da su a jihohin, Filato, Zamfara da Imo.
Olorogun Sleek Oshare, wani shugaban al'umma a jihar Delta, ya ce rikicin gona ne ya jawo aka kashe sojoji a jihar. Ya roki gwamnati da ta gudanar da sahihin bincike
Majalisar dattawa dattawa ta buƙaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta biya diyya ga iyalan sojojin da aka kashe a Delta tare da kamo wadanda suka aikata laifin.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari