ECOWAS: Shin Da Gaske Dakarun Mali Da Burkina Faso Sun Isa Nijar? Bayanai Sun Fito

ECOWAS: Shin Da Gaske Dakarun Mali Da Burkina Faso Sun Isa Nijar? Bayanai Sun Fito

  • Sojijin da su ka yi juyin mulki a Nijar sun yi fatali da barazanar kungiyar kasashen ECOWAS na wa’adin kawanaki bakwai
  • A ranar 30 ga watan Yuli, hafsoshin soji na ECOWAS sun amince da daukar matakin soji a Nijar cikin kwanaki bakwai
  • Duk da wannan barazana na kungiyar ECOWAS, sojojin Jamhuriyar Nijar sun kara samun karfi daga Mali da Burkina Faso

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yamai, Nijar – Rahotanni sun tabbatar da cewa sojoji daga Mali da Burkina Faso sun isa Jamhuriyar Nijar don taimakon sojin kasar.

A wani hoto da Hukumar Yada Labarai da Hulda da Jama'a ta kasar (DIPR) ta wallafa, an gano dakarun kasar Mali a Jamhuriyar Nijar.

Dakarun kasashen Mali da Burkina Faso sun dira a Jamhuriyar Nijar
An Bayyana Cewa Dakarun Kasashen Mali Da Burkina Faso Sun Isa Nijar. Hoto: @ali-naka.
Asali: Twitter

Idan ba a manta ba, an hambarar da Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli yayin da masu tsaronsa suka kifar da shi, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Nijar Ta Nada Shirgegen Mukami Yayin Da Kasar Ke Cikin Matsin Lamba Na Mika Mulki Daga ECOWAS, Bayanai Sun Fito

Gargadin kungiyar kasashen ECOWAS kan Nijar

Kungiyar kasashen ECOWAS wanda Shugaba Bola Tinubu ke jagoranta sun yi wata ganawa kwanaki bayan juyin mulkin inda suka ba wa sojojin kwanaki bakwai da su mika mulki ga Bazoum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasashe Mali da Burkina Faso sun goyi bayan juyin mulkin inda suke shirin tura dakaru don taimaka wa Jamhuriyar Nijar.

France 24 ta tattaro cewa wani daga cikin sojojin Mali ya na cewa:

“Burkina Faso da Mali za su tura sojoji zuwa Yamai don nuna musu goyon baya a matsayin ‘yan uwa.”

Nijar ta yi fatali da gargadin bayan Mali da Burkina Faso sun goyi bayansu

Kamar yadda ma’aikatar kasashen waje ta Nijar din ta tabbatar, dakarun za su iso Nijar a yau Litinin 7 ga watan Agusta.

Sojin da suka yi juyin mulkin sun yi fatali da kwanaki bakwai da kungiyar ECOWAS ta bayar don dawo da Bazoum kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sanar Da Ranar Da Za Ta Sake Zama Don Yanke Hukunci Kan Nijar

An kaddamar da juyin mulki a Mali a shekarar 2020 yayin da aka yi na Burkina Faso a 2022.

Sojojin Nijar Sun Yi Fatali Da Bukatar ECOWAS Na Su Mika Mulki A Mako 1

A wani labarin, sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun yi fatali da bukatar ECOWAS na su mika mulki ga Mohamed Bazoum.

Kungiyar kasashen ECOWAS a makon da ya gabata ta ba wa sojojin wa'adiin mako daya da su mika mulki ko su fuskanci takunkumi.

Sun yi watsi da gargadin tare da jan kunnen kungiyar ECOWAS da kada su kuskura su yi amfani da karfin soji a kan kasar Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel