Nijar, Mali, Burkina Faso, Da Guinea Ba Su Halarci Taron Shugabannin Tsaro Na ECOWAS Ba

Nijar, Mali, Burkina Faso, Da Guinea Ba Su Halarci Taron Shugabannin Tsaro Na ECOWAS Ba

  • A ranar Laraba ne shugabannin tsaron ƙasashen ECOWAS suka gudanar da taro a hedikwatar tsaron Najeriya da ke Abuja
  • Shugabannin tsaron sun taru ne domin tattauna batutuwan da suka shafi juyin mulkin da sojoji suka yi a jamhuriyar Nijar
  • Taron ya samu halartar ƙasashe 10 daga cikin ƙasashe 15 da suka kasance mambobin ƙungiyar ta ECOWAS

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - An bayyana cewa shugabannin tsaron ƙasashen Mali, Nijar, Burkina Faso, Guinea da Guinea Bissau ne ba su halarci taron shugabannin tsaro na ƙasashen ECOWAS da ya gudana a Abuja ba.

Shugaban tsaron Najeriya, Manjo Janar Christopher Musa ne ya jagoranci taron shugabannin tsaron ƙasashe 15 na ECOWAS, a hedikwatar tsaron Najeriya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Taron shugabannin tsaro na ƙasashen ƙungiyar ECOWAS
Kasashe 5 da suka haɗa da Mali da Burkina Faso ba su halarci taron shugabannin tsaro na ƙasashen ECOWAS ba. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

An tattauna batun juyin mulkin da ya faru a Nijar

Kara karanta wannan

Nijar: ECOWAS Ta Tura Wakilanta Don Tattaunawa Da Sojojin Da Suka Kifar Da Gwamnatin Bazoum

Shugabannin tsaron na soji dai sun tattauna ne kan batutuwan da suka shafi juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai a wajen taron ba a ga giccin ko ɗaya daga cikin shugabannin tsaron waɗannan ƙasashe biyar ba wanda hakan ke nuna ƙin amincewarsu kan matsayar da ECOWAS ta cimmawa a kan Nijar.

Shugabannin tsaron dai na tattauna matakan da ya kamata su ɗauka kafin cikar wa'adin kwana bakwai da ECOWAS ta bai wa sojojin Nijar na su mayar da mulki hannun fararen hula.

Ƙasashen da suka halarci taron shugabannin tsaron

Ƙasashen da suka halarci taron shugabannin tsaron da ya gudana ranar Laraba a Abuja sun haɗa da Najeriya, Benin, Togo, Ghana, Sanagal, Saliyo, Laberiya, Gambia, Kwaddibuwa, da kuma ƙasar Cabo Verde.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai kungiyar raya tattalin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), suka bai wa sojojin Nijar wa'adin kwanaki bakwai kan su mayar da mulki hannun Bazoum kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Fara Shawo Kan Shugabannin Kwadago a Taron Villa, Bayanai Sun Fito

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ƙara da cewa a shirye ECOWAS take ta yi amfani da ƙarfin soja wajen dawo da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Ministan Buhari ya ja kunnen Tinubu dangane da juyin mulkin Nijar

Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan gargaɗin da tsohon minista a gwamnatin Buhari, Abdulrahman Dambazau ya yi wa Tinubu dangane da juyin mulkin Nijar.

Dambazau wanda shi ne tsohon hafsan hafsoshin Najeriya, ya ce Najeriya za ta iya fama da 'yan gudun hijira idan ba a yi abinda ya kamata ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng