Juyin Mulki: Shehu Sani Ya Ce Da Wuya Ne Tawagar ECOWAS Ta Yi Nasarar Dawowa Da Bazoum Mulkinsa

Juyin Mulki: Shehu Sani Ya Ce Da Wuya Ne Tawagar ECOWAS Ta Yi Nasarar Dawowa Da Bazoum Mulkinsa

  • Sanata Shehu Sani ya yi tsokaci kan tawagar ECOWAS da Abdulsalami Abubakar ya jagoranta zuwa Nijar domin sasanci
  • Ya ce yana da yakinin cewa tawagar za ta iya cin nasara wajen sanyawa a saki Bazoum
  • Sai dai Shehu Sani ya ce ba ya tunanin cewa tawagar ta ECOWAS za ta yi nasarar dawowa da Bazoum kujerarsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi hasashen sakamakon da tawagar diflomasiyya ta kungiyar ECOWAS za ta iya samu a zuwan da ta yi jamhuriyar Nijar.

Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar ne ke jagorantar tawagar zuwa Nijar, biyo bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a makon da ya gabata.

Shehu Sani ya hasaso abinda zai faru a zuwan da tawagar ECOWAS ta yi Nijar
Shehu Sani ya ce tawagar ECOWAS ba za ta iya dawo da Bazoum kan kujera ba. Hoto: Shehu Sani(Facebook)/Adam Abu-bashal/Anadolu Agency via Getty Images
Asali: UGC

Shehu Sani ya yaba da matakin da aka dauka

Shehu ya ce matakin na diflomasiyya abin a yaba ne matuka, kuma yana da kwarin gwiwar cewa tawagar za ta magance matsalar da ake fuskanta a yanzu a Nijar.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta.

Shehu ya ce tawagar ta su Abdulsalami za ta iya samun nasara wajen sanyawa a saki hambararren shugaban ƙasar Muhammed Bazoum.

Sai dai ya ce ba ya tunanin cewa tawagar ta ECOWAS za ta yi nasarar dawo da Bazoum kan karagarsa ta mulki.

ECOWAS: Sultan ya raka Abdulsalami zuwa Nijar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan cewa mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya raka Janar Abdulsalami Abubakar zuwa jamhuriyar Nijar domin yin sasanci.

Hakan dai ya biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka gudanar a ƙasar gami da tsare hamɓararren shugaban ƙasar Muhammed Bazoum.

Kasashe 5 da ba su halarci taron shugabannin tsaro na ECOWAS ba

Kara karanta wannan

Tantance Ministoci: ‘Yar Katsina ta Sharba Kuka Gaban Sanatoci da Tuna Mahaifinta

Legit.ng ta kawo muku cewa a ranar Laraba, 2 ga watan Agusta ne shugabannin tsaro na kasashen ECOWAS suka gudanar da taro a hedikwatar tsaro ta Najeriya da ke Abuja.

Sai dai a cikin kasashe 15 da suka kasance mambobi na ECOWAS, guda 10 ne suka halarci taron, yayin da shugabannin tsaron kasashe 5 suka ki halarta.

An gudanar da taron ne don tattaunawa kan yadda za a bullowa lamarin juyin mulki da sojojin suka yi wa gwamnatin Bazoum na jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel