‘Yan Bindiga Sun Ji Luguden Wuta, Sun Fara Rokon Ayi Sulhu da Gwamnatin Najeriya

‘Yan Bindiga Sun Ji Luguden Wuta, Sun Fara Rokon Ayi Sulhu da Gwamnatin Najeriya

  • Dakarun Operation Hadarin Daji sun matsawa ‘yan bindiga lamba, sun rasa inda za su kan su a yau
  • ‘Yan ta’addan da ke ta’adi a Arewa maso yamma sun sha lugude a Tsafe, Faskari, Jibia da Zurmi
  • Zuwa yanzu shugabannin miyagun sun fara tunanin yadda za a lallabi gwamnati domin ayi sulhu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zamfara - Ganin yadda dakarun sojojin saman Najeriya su ke ragargazar ‘yan bindiga ya fara tada hankalin miyagun ‘yan ta’addan da ke yankin Arewa.

Rahoton da ya fito daga PRNigeria ya nuna gawurtattun ‘yan bindigan da su ka addabi Arewa maso yamma su na neman yadda za a tsagaita wuta.

Jagororin ‘yan ta’addan a jihohin Zamfara da Katsina sun aika da wakilai zuwa wani taro da aka yi a kauyen Gusami da ke birnin Magaji a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Jawowa El-Rufai, Danladi Da Okotete Samun Tasgaro a Zama Ministoci

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga su na neman sulhu Hoto: @MNIJJ
Asali: Twitter

Jagororin 'Yan bindiga sun hadu a Zamfara

Wadanda su ka halarci taron sun da jagororin ‘yan ta’addan ko kuwa wadanda su ka wakilce su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

D/Nigerian ta ce taron ya samu albarkar Usman Ruga Kachallah, Alaji Shingi, Lauwali Dumbulu, Shehu Bagiwaye, Shehu Karmuwal da Jarmi Danda.

Makasudin zaman da su ka yi wa karamar hukumar Birnin Magaji shi ne su hada-kai, su nemi yadda za su nemi ayi sulhu da gwamnatin Najeriya.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigan sun yi alkawarin ajiye makamansu idan aka sasanta da hukuma, ganin lahanin da sojoji su ka yi masu a kwanakin nan.

"Sun hadu ne domin ganin yadda za su dunkule, su nemi a sasanta da gwamnati bayan sojoji sun jikkata su a wasu manyan hare-hare.
Sun dauki alkwarin ajiye makamansu domin ayi sulhu, sun kuma yi nadamar abin da ya faru, za su bi sababbin gwamnatocin jihohinsu."

Kara karanta wannan

Ku Yi Hakuri: Shugabannin 'Yan Bindiga a Arewa Sun Nemi Afuwa, Za Su Ajiye Makamai

- Majiyar tsaro

'Yan bindiga sun ji haza

Leadership da ta fitar da irin rahoton ta je ‘yan bindigan da aka sani da ta’adi a wasu jihohi, sun rasa kwarin gwiwarsu a watannin baya-bayan nan.

Luguden wutan da sojoji su ke yi wa miyagun ya taba gidaje, iyali, dangi, dabbobi, wuraren ajiye da duk wasu mafakar da su ke labewa a cikin jeji.

Bayan luguden wuta da aka yi a yankunan Tsafe, Faskari, Jibia da Zurmi, a shirye su ke ayi amfani da kungiyoyi irinsu Miyetti Allah domin a sasanta.

Arewa sai godiya - Hadimin Tinubu

Dazu aka rahoto Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz ya ce ko yanzu shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba maras ɗa kunya wajen mukamansa.

Idan aka bar zancen ministocin da Arewa sun fi kowa samun kujeru, shugaban Najeriya ya dauko Sakataren gwamnatin tarayya daga Benuwai a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel