Labarin Sojojin Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cafke miyagu takwas da ake zargi aikata manyan laifuffuka a jihar Filato dauke da tarin makamai, ana neman wasu ruwa a jallo.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Laftanar Janar Christopher Musa, ya umarci kwamandojin da ke yaki da satar man fetur su kawo karshen matsalar nan da mako biyu.
Majalisar wakilai ta gayyaci wasu daga cikin shugabannin tsaron Najeriya su mata bayani bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya ba sojoji umurnin fara noma.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci babban hafsan tsaro na kasa ya tabbatar ya kawo karshen satar mai da fasa bututun mai cikin kankanin lokaci.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kubutar da wasu mutum 57 da 'yan ta'addan Boko Haram suka sace a dajin Sambisa. Sojojin sun kuma hallaka 'yan ta'adda.
Hedikwatar tsaro ta DHQ a jiya Alhamis ta ce sojoji sun dakile shirin da ‘yan ta’adda ke yi na lalata wasu muhimman kadarorin Najeriya. DHQ ta yi karin haske.
Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan yan ta'adda a karamar hukumar Lau ta jihar Taraba, ta ceto mata biyu, yan bindiga sun kashe juna a yankin Wukari.
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato sun nuna cewa ƴan bindiga sun hallaka mataimakin kwamandan rundunar sojin Operation Save Haven.
Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar hallaka yan ta'adda a jihohin Anambara, Katsina da Oyo. Ta kwato tarin makamai da kama dan ta'addan da ake nema ruwa a jallo.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari