Dakarun Sojoji Sun Ragargaji Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Makamai Da Babura

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Makamai Da Babura

  • Rundunar sojin kasan Najeriya ta ce ta samu nasarar fatattakar wasu 'yan bindiga daga dajin karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna
  • A yayin sumamen da dakarun sojin suka yi, sun yi nasarar kwato makamai da babura daga hannun 'yan ta'addan
  • Wani sumame na daga cikin shirin sojojin Najeriya na kakkabe duk wasu 'yan ta'adda da ke buya a dazukan jihar Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Tawagar farko ta rundunar sojin kasan Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kwato makamai da babura a hannun 'yan ta'adda a jihar Kaduna.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Musa Yahaya, mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar, ya tabbatar da nasarar farmakin.

Kara karanta wannan

Sojin sama sun yi ajalin kasurgumin dan ta'adda, Kachalla, sun hallaka kwamandojin Dogo Gide 3

Sojoji sun kwato makamai da babura daga hannun 'yan ta'adda a Kaduna
Dakarun sojin kasan Najeriya sun yi nasarar kwato makamai da babura a hannun 'yan ta'adda a jihar Kaduna. Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Yahaya ya ce kwato kayayyakin na daga cikin yunkurin sojoji na kakkabe duk 'yan ta'addan da ke cikin dajin Kaduna, The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hare-hare biyu da sojoji suka kai wa 'yan ta'adda a dajin Kaduna

Ya ce dakarun sun farmaki 'yan ta'addan bayan samu rahotannin sirri, inda suka yi hadin guiwa da 'yan sa kai tare da yi wa 'yan ta'addan kwantan bauna a Dogon Dawa-Damari, a karamar hukumar Igabi.

Yahaya ya kara da cewa 'yan bindigar sun ranta a na kare cikin kidimewa sakamakon ruwan harsasan da suka sha daga dakarun sojin.

Kamfanin dillacin labarai ya ruwaito Yahaya yana cewa:

"Dakarun sojin sun yi rangadi a dajin inda suka kwato 'bareta pistol', bindigar AK-47 guda daya da kuma kwafsan harsasan bindigar AK47 guda daya.
"Haka zalika, sojojin sun samu rahoton gilmawar 'yan bindiga a Kwanar Mutuwa da ke Birnin Gwari, inda suka yi musayar wuta da ya tilasta 'yan bindigar tserewa."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fatattaki shugaban karamar hukuma a jihar Niger, ta fadi dalili

Jaridar Vanguard ta ruwaot jami'in hulda da jama'a na rundunar sojin ya na cewa a farmakin Kwanar Mutuwa ne sojoji suka kwato babura daga hannun 'yan ta'addan.

Tinubu ya ja wa sojoji kunne, "kar ku kara kai hari kan farar hula"

A wani labarin, shugaban kasa Bola Tinubu ya gargadi sojojin Najeriya da su kauracewa farmakar farar fula da kuma sauran hukumomin tsaro a kasar, Legit Hausa ta ruwaito.

Tinubu na martani kan harin bam da sojojin suka kai wa masu maulidi a Tudun Biri, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna inda akalla mutum 100 suka mutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel