Dakarun Sojoji Sun Sheke Manyan Kwamandojin Yan Ta'adda 4, An Bayyana Sunayensu

Dakarun Sojoji Sun Sheke Manyan Kwamandojin Yan Ta'adda 4, An Bayyana Sunayensu

  • Dakarun sojoji sun samu nasarar tura manyan kwamandojin ƴan ta'adda mutum huɗu a wasu hare-hare
  • A wata sanarwa da hedikwatar tsaro ta fitar, ƴan ta'addan da aka sheƙe sun yi ƙaurin suna wajen halaka mutane da yin garkuwa da su
  • Machika, Haro, Dan Muhammadu da Ali Ahaji Alheri su ne kwamandojin ƴan ta'addan da suka baƙunci lahira

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta tabbatar da kashe wasu fitattun kwamandojin ƴan ta'adda huɗu a hare-haren da aka kai ta sama cikin mako guda.

Jaridar Daily Trust ta ce ƴan ta'addan da suka baƙunci lahira sun haɗa da Haro. Dan Muhammadu, Ali Alhaji Alheri wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje da Machika.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Matasa marasa aikin yi sun aike da sako mai muhimmanci ga ministar Tinubu

Dakarun sojoji sun halaka kwamandojin yan ta'adda
Kwamandojin yan ta'adda hudu sun sheka barzahu a hare-haren dakarun sojoji Hoto: @NigerianArmy
Asali: Twitter

Darakta mai kula da ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 16 ga watan Disamba a Abuja, cewar rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buba ya bayyana cewa Machika babban ƙwararren mai haɗa bam na ƴan ta'adda ne kuma ƙanin fitaccen ɗan ta’adda (Dogo Gide) yayin da Haro da Dan Muhammadu suka ƙware wajen yin garkuwa da mutane.

Ta yaya aka kashe ƴan ta'addan?

Ya yi nuni da cewa, a wani farmakin haɗin gwiwa tsakanin sojojin sama da na ƙasa da suka kai hari a ranar 11 ga watan Disamba, sun kashe Kachalla Kawaje, fitaccen shugaban ƴan ta’addan da ya yi garkuwa da daliban jami’ar tarayya ta Gusau, Zamfara.

Ya ƙara da cewa an kashe Kachalla ne a ƙaramar hukumar Munya ta Nijar tare da wasu dakarunsa.

Kara karanta wannan

Wike ya shiga matsala yayin da ake zarginsa da aikata wani mummunan laifi

A cewarsa, sojoji suna ƙara tunkarar wasu ƴan ta'addan, kuma za su fuskanci irin abin da ya auku da su Kachalla.

Ya ƙara da cewa harin da aka kai ya yi sanadin kashe kwamandojin ƴan ta’adda sama da 38 da dakarunsu, yayin da aka kama wasu ƴan ta'adda 159.

Sojoji za su cigaba da farautar ƴan ta'adda

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Dakarun sojoji na cigaba da farautar shugabannin ƴan ta'adda da fatattakarsu a duk inda suke ɓoyewa."
"Sojoji za su cigaba da yin yaƙi da ƴan ta'adda da ƴan barandarsu har sai an halaka su ko sun miƙa wuya."

Matawalle Ya Yabi Dakarun Sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Muhammad Matawalle ya yaba wa dakarun sojoji kan kisan ƴan bindiga.

Matawalle ya yi yabon ne bayan dakarun sojojin sun halaka tantiran ƴan ta'adda mutum 30 a jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng