Zaman Sirri: Abin da Shugaban Hafsun Tsaro Ya Fadawa Malamai Kan Kashe Masu Maulidi

Zaman Sirri: Abin da Shugaban Hafsun Tsaro Ya Fadawa Malamai Kan Kashe Masu Maulidi

  • Manyan malaman addinin Musulunci sun hadu da Hafsun tsaron Najeriya watau Christopher Musa a makon nan
  • Sojoji sun nemi zama da Shehunai daga garuruwan Arewacin Nejeria a dalilin mutane kimanin 100 da aka kashe
  • An samu tsautsayi jirgin soja ya jefa bam-bamai ga wasu da ke yin taron Mauludi cikin dare a kauyen Tudun Biri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Manyan malaman addinin musulunci sun zauna da shugaban hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa a makon nan.

Aminiya ta ce zaman ya biyo bayan hadarin da ya auku a garin Tudun Biri, inda sojojin kasa su ka kashe mutane kimanin 100.

Shugaban Hafsun Tsaro
Hafsun Sojoji da malamin addini Hoto: aminiya.ng
Asali: UGC

Kuskuren sojoji ne ko ba kuskure ba?

Kara karanta wannan

Idan aka halatta shigo da shinkafa, siminti da sauransu, farashinsu zai sauko – Bankin duniya

Kisan da sojoji su ka yi wajen taron maulidi ya jawo fushi a Najeriya, har wasu malamai suna zargin cewa harin ba kuskure ba ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Christopher Musa ya fadawa malaman addinin musuluncin cewa sun fara gudanar da cikakken bincike a kan abin da ya faru.

Shugaban sojojin na Najeriya ya dauki alkawari cewa hukuma za ta dauki matakin da ya dace kamar yadda malamai su ke ta yin kira.

"Sojoji ba za su sake yin irin haka ba"

Mai magana da yawun bakin sojojin kasa Birgediya Janar Tukur Gusau ya ce za su dage domin ganin hakan bai maimaita kan shi ba.

Da yake jawabi bayan taron, Janar Gusau ya nuna ba su da buri a kasa da ya wuce tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sheikh Bashir Aliyu Umar ya jagoranci malamai

Kara karanta wannan

Manyan hare-hare 8 da sojoji suka kai wa farar hula ta sama a cikin shekaru 6 a Najeriya

Rahoton ya ce Dr. Bashir Aliyu Umar OON ne ya jagoranci malaman zuwa wannan zama da aka yi da hafsun tsaro a birnin Abuja.

Babban malamin hadisin ya yabi Janar Musa ganin yadda ya tausayawa al’ummar Tudun Biri, ya ziyarce su da jin labarin abin ya faru.

Bashir Aliyu ya yi kira ga dakarun sojoji su lura da halin kuncin da al’umma su ke ciki.

Wasu nalamai sun soki Sojoji

Kwanakin baya aka ji Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yana zargin cewa abin da ya faru a kauyen Tudun Biri ba kuskure ba ne.

Dr. Gumi ya ce ba wannan ne karon farko da sojoji su ka yi ikirarin kashe mutane bisa kuskure ba, kuma a ko yaushe a yankin Arewa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel