Labarin Sojojin Najeriya
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bukaci sojoji da su kara kaimi wajen kakkabe 'yan ta'adda da 'yan bindiga wadanda suka addabi wasu yankunan jihar.
Heditkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta sanar da cewa dakarun sojoji a fadin kasar nan halaka 'yan ta'adda 254 tare da cafke wasu 264 a yayin samame daban-daban.
Dakarun sojoji na Operation Safe Haven da ke aikin samar da zaman lafiya a jihar Olateau, sun yi nasarar gano wata masana'anta inda ake kera muggan makamai a jihar.
Wani sojan Najeriya da ya samu rauni a fagen daga yayin kare martabar Najeriya, ya soki matakin Tinubu na ba 'yan wasan Super Eagles kyaututtuka masu gwabi.
Jami’an tsaron Najeriya sun yanke shawarar yin amfani da lambar tantancewa ta kasa (NIN) da kuma lambar BVN wajen zakulo masu aikata laifuka da kuma kama su.
Majalisar dattawan Najeriya ta shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro a zauren majalisar da ke Abuja, kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kasa.
A wani yunkuri na dakile hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa wasu garuruwa a jihar Filato, Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da kafa wani sansanin sojoji a jihar.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taso a jirgin sama daga birnin tarayya Abuja zuwa jihar Kaduna domin halartar taron cikar makarantar sojoji NDA shekara 60.
Dakarun sojoji na Bataliya ta 93 da ke a jihar Taraba, sun samu nasarar cafke wata mata da ake zargi da yin garkuwa da mutane, yayin karbar kudin fansa.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari