"Ba a Kyauta Mana": Soja Ya Fusata Kan Kyautar da Tinubu Ya Yi Wa 'Yan Wasan Super Eagles

"Ba a Kyauta Mana": Soja Ya Fusata Kan Kyautar da Tinubu Ya Yi Wa 'Yan Wasan Super Eagles

  • An soki shugaban ƙasa Bola Tinubu kan karramawar da ya yi wa ƴan wasan Super Eagles saboda rawar da suka taka a gasar cin kofin nahiyar Afirika
  • Wani soja ne ya soki shugaban ƙasan a shafukan sada zumunta inda ya nuna ɓacin ransa game da yadda ake ƙin yabawa da sadaukarwar da suke yi
  • Sojan ya yi iƙirarin cewa ya samu raunin harbin bindiga lokacin da yake yi wa Najeriya hidima a fagen yaƙi yayin da ya fitar da hoton raunin da ya samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wani sojan Najeriya mai suna Adie Paul ya soki matakin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka na bai ƴan wasan Super Eagles kyaututtuka.

Shugaban ƙasar dai ya ba su kyautar gidaje da filaye da kuma lambar yabo ta ƙasa saboda sun zo na biyu a gasar cin kofin ƙasashen nahiyar Afirika.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bayyana alfanun da aka samu sakamakon rufe rumbunan masu boye abinci

Soja ya caccaki Shugaba Tinubu
Shugaba Tinubu ya ba 'yan wasan Super Eagles kyaututtuka Hoto: @AfolabiBB
Asali: Twitter

Ya nuna rashin jin daɗinsa cewa sojoji da ke bakin aiki irin shi, ba sa samun irin wannan karramawa duk da sadaukarwar da suke yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa sojan yake yin ƙorafi?

Paul, wanda ya samu raunin harsashi a lokacin da yake aiki a yankin Arewa maso Gabas, ya bayyana takaicinsa a shafukan sada zumunta.

Ya rubuta cewa:

"Hatta Ahmed Musa wanda bai buga ƙwallo ko sau ɗaya a AFCON ba, ya sami gida, fili da OON. Lokuta masu ban al'ajabi.
"Duk da haka, a matsayina na soja, na zauna a Arewa maso Gabas ina yaƙi da Boko Haram har na tsawon shekara huɗu, an harbe ni, kuma har yanzu ina ɗauke da harsashin a jikina har zuwa yau, ba ko wata lambar yabo daga rundunar soji/gwamnatin Najeriya."

A ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu, Tinubu ya ba da lambar yabo ta ƙasa ta Member of the Order of Niger (MON) ga kowane daga cikin ƴan wasan tawagar Super Eagles da suka samu azurfa a AFCON 2023.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Amarya ta hallaka mijinta a jihar Neja

Tawagar ƴan wasan mutum 25 da masu horar da ƴan wasan an kuma basu kyautar filaye da gidaje kamar yadda Shugaba Tinubu ya bayyana.

Ahmed Musa Ya Aike da Saƙo Ga 'Yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa kyaftin ɗin tawagar ƴan wasan Super Eagles, Ahmed Musa, ya aike saƙo ga ƴan Najeriya bayan rashin nasarar da suka yi a wasan ƙarshe na gasar cin kofin AFCON 2023.

Tsohon ɗan wasan na ƙungiyar Kano Pillars ya yabawa ƴan Najeriya bisa sadaukarwa da goyon bayan da suka bayar a gasar AFCON 2023 da aka kammala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel