Labaran Duniya
Allah ya yi wa mahaifiyar mahaifiyar fitaccen dan wasan kwallon kafa na Brazil, Pele, Celeste Arantes rasuwa tana da shekara 101. Ta rasu a ranar Juma'a a Brazil.
Gwamnatin Tajikistan karkashin jagorancin Emomali Rahmon ta zartar da dokar da ta haramta mata sanya hijabi, da yara yin bukukuwan babbar Sallah.
Kungiyar gwagwarmaya ta Hezbollah da ke Lebanon ta ce duk wasu nau'in tsoratarwa da yada labaran yaki a Isra'ila da kawayenta ba zai girgiza su ba.
Bankin duniya ya kafawa Najeriya manyan sharudda kafin ya ba ta rancen dala biliyan 1.5. Bankin Duniya ya ce zai iya soke rancen kudin idan aka karya dokokin.
Hukumar FIU ta kasar India ta lafta tara kan kamfanin hada-hadar kirifto na Binance kan zargin safarar kudade. Hukumar ta ci kamfanin tarar Dala miliyan 2.25.
Gwamnatin India ta sanar da mutuwar mutane 36 da kuma sama da 100 da ke wance a asibiti bayan shan giya a yankin Kallakurichi da ke jihar Tamil Nadu.
Akalla ‘yan kasashen Jordan da Iran 19 ne suka mutu a lokacin aikin Hajji a kasar Saudiya sakamakon tsananin zafi. Ana kuma fargabar mutum 17 sun bace.
Bankin duniya ya gargadi gwamnatin Najeriya kan karin kudin ruwa da ake yi ga masu karbar bashi. Bankin ya ce karin kudin zai kara kawo tashin farashin kayayyaki.
Ministan kudi kuma ministan tattalin arziki, Wale Edun, ya ba da sanarwar amincewar Bankin Duniya na ba Najeriya bashin $2.25bn domin farfado da tattalin arziki.
Labaran Duniya
Samu kari