Wata Sabuwa: Jami'an Tsaro Sun Mamaye Wuraren da Aka Lika Fastoci da Allunan Tallata Tinubu

Wata Sabuwa: Jami'an Tsaro Sun Mamaye Wuraren da Aka Lika Fastoci da Allunan Tallata Tinubu

  • An tura jami’an tsaro domin kare fastoci da allunan tallata Shugaba Bola Tinubu a Kaduna gabanin ziyararsa da ake sa ran yi ranar Asabar
  • An shirya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC na 2027 a filin wasa na Kaduna Township Stadium
  • An gyara filin wasan mai ɗaukar mutum 8,000, inda aka yi masa fenti tare da ƙawata shi da tutocin APC da fastocin Tinubu da sauran ’yan siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - An ga jami’an tsaro suna gadin fastoci da allunan tallata Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a birnin Kaduna, gabanin ziyarar da ake sa ran zai kai jihar ranar Asabar, 24 ga Oktoba, 2026.

Matakin ya zo ne gabanin shirin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC na shekarar 2027 a Kaduna.

Kara karanta wannan

2027: Ana zargin wasu ƙusoshin APC sun fito da kudi don ruguza shirin hadewar yan adawa

Tinubu.
Wata Sabuwa: Jami'an Tsaro Sun Mamaye Wuraren da Aka Lika Fastoci da Allunan Tallata Tinubu
Source: Facebook

Jami'an tsaro na gadin fastocin Tinubu

Daily Trust ta ruwaito cewa an girke jami’an tsaro a muhimman wurare daban-daban na birnin domin hana lalata kayan tallan siyasar shugaban ƙasar.

Jami’an Hukumar Kula da Bin Dokokin Hanyoyi ta Jihar Kaduna (KASTLEA) da na Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) na cikin waɗanda aka ɗora wa alhakin kare fastoci da allunan tallan.

Jami'an tsaron sun mamaye wurare daban-daban musamman a manyan hanyoyin da suka doshi filin wasa na Kaduna Township Stadium, inda ake sa ran gudanar da gangamin.

An girke jami’an tsaro a Kaduna

Duk da cewa ba a samu amsa kai tsaye daga gwamnatin Kaduna ba, wani jami’in tsaro da aka tura aikin ya shaida cewa an zaɓi wasu jami’ai domin kare kayan tallan siyasar shugaban ƙasa daga yankin filin wasan Township Stadium har zuwa Kawo.

Jami’in ya ce an haɗa su da jami’an KASTLEA domin tabbatar da cewa ba a lalata allunan tallan da fastocin Tinubu kafin gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen ba.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano masu shirya kai farmaki kan matasan da za su y aikin zaɓen 2027

Ya ƙara da cewa aikinsu ya fi mayar da hankali kan dare, domin a lokacin ne matasa za su iya lalata kayan tallan.

Uba Sani.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani lokacin da ya shigo gangamin taron APC Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

A cewarsa, an ba su wannan aiki ne bayan rundunarsu ta fitar da wata takardar umarni da ke umartar wasu jami’ai da su samar da tsaro ga kayan tallan yaƙin neman zaɓen.

Jami’an sun kasance suna sa ido kan masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyoyin.

Haka kuma, an ga motocin sintirin ’yan sanda a kusa da wurin da ake sa ran gudanar da gangamin da kuma kan titin Ahmadu Bello Way, ciki har da mahadar da ke kusa da tsohon ofishin NEPA.

An kuma ga ’yan sanda ɗauke da makamai a kusa da mahadar da ke wajen Asibitin 44, yayin da shirye-shiryen tsaro ke ƙaruwa gabanin ziyarar.

Fastocin Tinubu da Abba sun mamaye Kano

Kun ji cewa fastocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, sun mamaye wasu muhimman wurare a birnin Kano.

An ga fastocin a kan titin State Road da ke kaiwa zuwa gidan gwamnatin Kano da fadar Nassarawa, inda Bayero yake zaune a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262