Babbar Magana: An Yi Barazanar Kashe Duk Wanda Ya Yi Magudi a Babban Zaben 2027

Babbar Magana: An Yi Barazanar Kashe Duk Wanda Ya Yi Magudi a Babban Zaben 2027

  • Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya yi barazanar kashe duk wanda ya yi maguɗin zaɓen 2027
  • Omo-Agege, wanda ke neman kujerar sanatan Delta ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, ya yi wannan barazanar a wani taron siyasa
  • Barazanar tasa ta zo ne kusan mako guda bayan Shugaba Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro su tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ovie Omo-Agege, ya yi barazanar cewa za a kashe duk wanda ya yi maguɗin zaɓen 2027.

Omo-Agege, wanda ke neman kujerar sanatan Delta ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, ya yi wannan barazanar ne a wani taron siyasa a mazabarsa.

Omo Agege.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ovie Omo-Agege Hoto: Ovie Omo-Agege
Source: Twitter

Barazanar kisa kan magudin zabe

Ya ƙara da cewa masu maguɗin zaɓe suna ƙoƙarin ƙwace makomar ’yan Najeriya da ta ’ya’yansu, yana mai gargaɗin cewa ba za su bari hakan ta faru ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda 'yunwa' za ta ruguza lissafin Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027

“Ina so in sake shiga labarai. Duk wanda ya yi maguɗin zaɓe, za mu kashe shi! Idan ba ka daraja rayuwarka, zo ka yi maguɗin zaɓen.
“Suna shirin maguɗi da makomarku, duuna shirin maguɗi da makomar ’ya’yanku. Muna jiransu, su gwada kawai, ko dai ka yi maguɗi ko ka mutu. Za mu yi musu irin abin da suka yi mana. A wannan karon babu zuwa kotu,” in ji Omo-Agege.

Omo-Agege ya fice daga APC

A watan Mayu, Omo-Agege ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar sanatan Delta ta Tsakiya a zaɓen shekarar 2027.

Ya sanar da ficewarsa daga APC ta wata wasiƙa mai kwanan wata 22 ga Mayu, wadda ya aikewa shugaban jam’iyyar na mazabar Orogun Ward 2, da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa a Jihar Delta.

A cikin wata sanarwa, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne bayan shafe makonni yana tattaunawa da abokan siyasa, magoya bayansa da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

An samu matsala: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya cire kansa daga shirin su Atiku a 2027

Tinubu ya umarci jami’an tsaro

Barazanar Omo-Agege ta zo ne kusan mako guda bayan Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da gudanar da zaɓen 2027 cikin ’yanci, adalci da sahihanci.

Ministan Tsaro, Christopher Musa, ne ya bayyana umarnin shugaban ƙasar yayin da yake yi wa manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayani bayan taron Majalisar Tsaro ta Ƙasa (NSC).

Musa ya ce shugaban ƙasar ya kuma umarci jami’an tsaro da su samar da yanayin da zai ba ’yan Najeriya damar amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya cikin kwanciyar hankali, ba tare da la’akari da jam’iyyar da suke goyon baya ba.

Kun ji cewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262