Kwankwasiyya
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta dage dokar hana fita da ta kafa a jihar a jiya Laraba 20 ga watan Satumba bayan yanke hukuncin kotun sauraran kararrakin zabe.
Jigon jam'iyyar NNPP, Alhaji Abbas Onilewura ya bayyana cewa son rai irin na Kwankwaso da neman mukamin APC shi ya jawo musu rashin nasara a kotu a Kano.
Shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas ya jagoranci murnan cin nasarar jam'iyyar a kotun zaben gwamnan jihar da ta bai wa Nasiru Gawuna nasara a yau.
An shiga wani irin yanayi a jihar Kano bayan yanke hukuncin kotu da ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir inda ta tabbatar da Nasiru Gawuna na APC a matsayin gwamna.
A yau Laraba, 20 ga watan Satumba, kotun zata yanke hukunci kan karar da Gawuna ya kalubalanci nasarar Abba Gida-Gida a zaben gwamnan jihar Kano.
Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamnan jihar Kano ta zabi ranar Laraba mai zuwa domin yanke hukunci kan sahihancin nasarar Abba Gida-Gida na NNPP.
Gwamnan jihar Kano ya bayyana daukar ma'aikatan da za su yi aikin don tabbatar da an kawo sauyi a lamarin tsafta a jihar. Ya dauki ma'aikata sama da 4500.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sallami kwamishinan Safiyo, Adamu Aliyu kan kkalamansa na barazana ga alkalan kotun zabe a jihar Kano kan zargin cin hanci.
Kwamishinan Safiyo a jihar Kano, Adamu Aliyu ya yi barazana ga alkalan kotun zabe a jihar inda ya ce za a shiga masifa idan alkalai su ka juya hukuncin kotun.
Kwankwasiyya
Samu kari