Kwankwaso Ya Karbi Bakuncin Mutum 17 Da Suka Samu Nasara a Zaben Majalisa

Kwankwaso Ya Karbi Bakuncin Mutum 17 Da Suka Samu Nasara a Zaben Majalisa

  • Jam'iyyar NNPP ta samu lashe kujerun majalisar wakilai da dama a zaben da ya gudana ranar 25 ga Febrairu
  • Hakazalika jam'iyyar ta kwace kujerun majalisar dattawa biyu cikin uku dake fadin jihar ta Kano
  • Jagoran jam'iyyar ya bayyana matukar farin cikinsa bisa wannan nasara duk da shi ya fadi zabe

Jagoran jam'iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP kuma wanda yayi mata takarar kujerar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karbi bakuncin sabbin zababbun majalisar dokokin tarayya.

Sabbin zababbun yan majalisar guda goma sha bakwai (17) sun samu nasara ne karkashin jam'iyyar a jihar Kano.

Sun ziyarci jagoran darikar Kwankwasiyyan ne a gidansa inda suka dauki hotuna tare da takardar shaidan samun nasara da hukumar INEC ta basu.

Daga cikinsu akwai wadanda suka taba zama a majalisa irinsu Alu Madakin Gini da kuma Abdulmumini Jibrin Kofa.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisa Ya Ki Karbar Satifiket Din INEC, Yana Harin Mukami Kusa da Tinubu

Majalsa
Mutum 17 Da Suka Samu Nasara a Zaben Majalisa Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya bayyana cewa yayi matukar farin ciki bisa nasarar da suka samu kuma yana kyautata zaton zasu sake samun karin kujeru a sauran zabukan da suka rage.

Ya bayyana hakan a jawabi da hotunan da ya daura a shafinsa na Tuwita yau Juma'a, 10 ga watan Maris, 2023.

A cewarsa:

"Na yi farin cikin karban bakuncin mutum 17 zababbun yan majalisar wakilan tarayya daga Kano, karkashin jam'iyyar NNPP, kuma sun gabatar min da takardar shaidarsu."
"Yayinda akwai sauran zabukan da ba'a kammala ba, da kuma zabukan gwamnoni da yan majalisun jihar, ina kyautata zaton jam'iyyarmu zata cigaba da samun karbuwa a fadin kasa."
"Ina taya sabbin yan majalisun muta kuma ina kira garesu su cika alkawuran da suka yiwa mutane."

Kalli hotunan:

Mambobin Jam'iyyar NNPP Sun Fito Zanga-Zanga Kan Sabon Sakataren INEC dake Kano

Kara karanta wannan

"Ta Ji Min Rauni A Maraina": Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyanawa Kotu

A jiya Mambobin jam'iyyar adawa ta New Nigeria Peoples Party, NNPP, a jihar Kano sun fito zanga-zanga kan zargin cewa Sakataren hukumar zabe INEC na jiha ya hada kai da jam'iyyar APC.

Wannan sakatare na hukumar INEC da ake zanga-zanga a kansa sunansa Alh. Garba Lawan Muhammad.

Freedom Radio ta ruwaito cewa masu zanga-zangar na zargin Alhaji Lawan ya hada kai da jam'iyyar APC dake kan mulki don yin magudi a zaben gwamnan jihar.

An yi zanga-zanga ne gaban hedkwatar hukumar INEC dake Kano.

Zaben gwamnan jihar Kano da sauran gwamnonin Najeriya zai gudana ne ranar 11 ga Maris, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel