Rabiu Kwankwaso Ne Magajin Buhari, In Ji Dan Gidan El-Rufai

Rabiu Kwankwaso Ne Magajin Buhari, In Ji Dan Gidan El-Rufai

  • Bashir Elrufai, ya bayyana Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin wanda zai gaji farin jinin Shugaba Muhammadu Buhari bisa ga dukkan alama
  • Bashir ya yi martanin ne kan masu yi wa Kwankwaso gori da 'shugaban kasar Kano' inda ya ce a shekaru kadan ba za su yi dariyar ba
  • Kwankwaso dai ya yi na hudu a zaben shugaban kasa da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu wanda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lashe

Bashir, daya daga cikin yayan gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yace dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso shi zai zama ''magajin Shugaba Muhammadu Buhari.''

Bashir El-Rufai
Rabiu Kwankwaso Ne Magajin Buhari, In Ji Bashir Elrufai. Hoto: @BashirElRufai
Asali: Twitter

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zo na hudu a zaben shugaban kasa da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 wanda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC ya lashe.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: An Fallasa Ɗan Takarar Shugaban Kasan da Peter Obi Ya Yi Wa Aiki a Zaɓen 2023

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP yazo na biyu yayin da Peter Obi na jam'iyyar Labour ya yi na uku.

Kwankwaso ya lashe zaben a iya Jihar Kano, inda ya samu kuri'a 997,279, wanda ya sa wasu yan adawar sa ke masa lakabi da 'Shugaban kasar Kano'.

Da ya ke martani a shafinsa na Twitter, Bashir ya bayyana cewa:

''Masu yi wa kwankwaso dariya da cewa shugaban kasar Kano ba za su yi dariyar ba nan da wasu shekaru. Shine zai gaji Buhari, ga dukkan alamu.''

Dan gwamnan na Jihar Kadunan dai ya shahara wajen bayyana ra'ayinsa a shafukan sada zumunta.

Yayansa, Bello, shine ya lashe zaben majalisar wakilai na tarayya don wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa.

Bello, wanda ya yi takara a jam'iyyar APC ya kada Samaila Suleiman, wanda shine dan majalisa mai ci a majalisar wakilai ta tarayya.

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: Allah Ya Yiwa Shahrarren Dan Kwangila a Jihar Kano, Alhaji Sani Dahiru Yakasai, Rasuwa

Samaila ya koma jam'iyyar NNPP bayan rasa tikitin takararsa a jam'iyyar APC bayan Bello ya kada shi zaben fidda gwani.

Martanin wasu masu amfani da shafin Twitter

@gboyegab ya ce:

"Eh yana da magoya baya sosai a Kano amma farin jinin Buhari a dukkan arewa ne baki daya, bana tabbacin RMK zai zamu hakan, amma lokaci zai bayyana."

@Chinedumakarant3

"Idan Kwankwaso ne Buhari na gaba, hakan na nufin zai fadi zaben shugaban kasa sau uku a jere nan gaba kamar Buhari kafin daga karshe ya zama shugaban kasa. Yanzu Kwankwaso ya rasa zabe 1, saura biyu nan gaba."

@KB_Ozee cewa ya yi:

"Na sha fada wa matasa masu fatan shiga siyasa su rika lura da abin da zai faru da Kwankwaso nan gaba kuma yana da buri a gaba bisa tsari."

Asali: Legit.ng

Online view pixel