Kwankwasiyya
Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa Kotun Koli ta tabbatar da Agbu Kefas matsayin zababben gwamnan jihar Taraba, ta yi watsi da karar NNPP .
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya isa jihar Kano a yammacin Laraba, 24 ga watan Janairu. Zai gana da masu ruwa da tsaki a APC a ranar Alhamis.
Rundunar yan sanda reshen jihar Kano ta ce ba zata yarda da duk wani rikici da zai kawo barazana ga zaman lafiya a jihar ba, CP Gumel ya kai ziyara Gaya.
Tsohon ɗan takarar PRP, Salihu Tanko Yakasai, watau Ɗawisu ya buƙaci Gwamna Abba Kabir ya kama tsohon kwamishinasa da ya yi barazanar kashe alkalai.
Gwamnatin jihar Kano ya bayyana dalilin ware makudan kudade a bangaren ilimi don inganta rayuwar al'ummar jihar da sauran bangarori masu muhimmanci.
Buba Galadima ya fadi yadda aka yaudari mutane da addini da tikitin Musulmi da Musulmi. Jagoran NNPP yace babu wanda ya san halin ‘dan siyasa kamar abokinsa.
Kotun Majistare da ke jihar Kano ta ba da umarnin tsare fitaccen dan siyasaa Kano Dan Bilki Kwamanda kan neman ta da husuma da cin zarafin Kwankwaso.
Wani sojan baka a siyasar Kano, Dan Bilki Kwamanda, ya ce nan ba da dadewa ba za su kawo karshen siyasar jagoran NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso..
Jam'iyyun adawa da suka hada da PDP da NNPP sun caccaki shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje kan kalamansa cewa matsalar zabe ba INEC ba ne illa 'yan siyasa.
Kwankwasiyya
Samu kari