Ganduje Ya Roki Gwamnan Jihar Kano Abba Gida-Gida Ya Shigo Jam’iyyar APC

Ganduje Ya Roki Gwamnan Jihar Kano Abba Gida-Gida Ya Shigo Jam’iyyar APC

  • Abdullahi Umar Ganduje ya roki gwamnan Kano ya bar jam’iyyarsa ta NNPP domin ya shigo APC mai-ci
  • Tsohon gwamnan Kano shi ne mai jagorantar APC-NWC, yace suna neman harin karin gwamnonin adawa
  • Dr. Abdullahi Ganduje ya aika goron gayyata zuwa ga Abba Kabir Yusuf ne wajen taron APC na reshen Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga Alhaji Abba Kabir Yusuf ya shigo jam’iyya mai mulki.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana so magajinsa ya yi watsi da NNPP, Daily Nigerian ta fitar da wannan rahoto a yammacin yau.

Abba da Ganduje
APC: Gwamnan Kano da Abdullahi Ganduje Hoto: Abba Kabir Yusuf, Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

Ganduje ya zauna da APC ta Kano

Tsohon gwamnan na Kano ya yi wannan magana ne a wajen taro masu ruwa da tsaki na APC da aka gudanar a Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje ya yi magana kan yiwuwar Kwankwaso ya koma jam'iyyar APC su sake haɗuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Alhamis dinna, Abdullahi Ganduje ya yi zama da jagororin jam’iyyar APC bayan shigowarsa garin Kano a jiya.

Meyasa Ganduje yake jawo Abba?

Ganduje yace sauya-shekar Abba Kabir Yusuf daga NNPP mai alamar kayan marmari zai Kano ta koma inuwa guda.

Idan wannan lamari ya tabbata, za a karasa gurgunta jam'iyyar PDP wanda ba ta numfashi da kyau a reshen Kano.

Shugaban na APC yana so kafin zaben 2027, jiharsa ta zama karkashin jam’iyya mai-mulki da rinjaye a majalisar tarayya.

Ganduje ya bayyana cewa APC mai adawa yanzu a jihar Kano ta yanke shawarar ta hada-kai da sauran kananan jam’iyyu.

Abba Gida Gida a jam'iyyar NNPP

Shugaban APC na kasan ya yi alkawarin ba gwamna Abba da magoya bayansa damar wanke allonsu idan suka shigo cikinsu.

A cewar tsohon gwamnan na Kano, sun yi nasarar jawo wasu gwamnonin jihohin adawa wanda kwanan nan za su tsallako.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya maida martani ga Ganduje kan roƙon sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC

"Idan mun yi haka a mataki na kasa, me zai hana muyi wannan a matakin jiha?"
"Kofarmu a bude ta ke sosai. Muna kira ga masu son shigowa jam’iyyar (APC)."
"Muna aika gayyata na musamman ga gwamnan Kano ya bar jam’iyyarsa ta NNPP, ya shigo APC"

- Abdullahi Umar Ganduje

APC: Sakon Dansarauniya ga Ganduje

Rahoton nan ya zo cewa Muazu Magaji yana zargin cewa wasu mutum ukun su ne suka kayar da APC a zabukakn 2019 da 2023.

Tsohon 'dan takaran gwamnan wanda ya bijirewa zaman da aka yi, ya kawo shawarar a jawo Kwankwasiyya da NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel