Abin Ya Yi Wa Ganduje Yawa Yayin da Ya Sake Shiga Uku Kan Kalamansa, PDP da NNPP Sun Yi Martani

Abin Ya Yi Wa Ganduje Yawa Yayin da Ya Sake Shiga Uku Kan Kalamansa, PDP da NNPP Sun Yi Martani

  • Kalaman shugaban jam'iyyar APC, Umar Ganduje ya jefa shi cikin matsala yayin da ya ke shan suka
  • Jam'iyyun adawa a kasar sun caccaki shugaban jam'iyyar da cewa shi ne babban matsalar dimukradiyya
  • Wannan na zuwa ne bayan Ganduje ya ce babbar matsalar zabe ba INEC ba ne illa 'yan siyasa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya sake jefa kansa a matsala kan kalamansa.

Idan ba manta ba, Ganduje a kwanakin baya ya ce babbar matsalar zabe a kasar 'yan siyasa ne ba hukumar INEC ba.

Ganduje ya sake shiga matsala kan kalamansa ga 'yan siyasa
Jam'iyyun adawa sun caccaki Ganduje kan kalamansa. Hoto: Abdullahi Ganduje.
Asali: Facebook

Mene ake cewa kan kalaman Ganduje?

Wannan kalaman na Ganduje ya jawo masa martani mai zafi daga jam'iyyun adawa da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon hadimin Buhari ya bayyana abun da dinkewar Kwankwaso da Ganduje ke nufi ga PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai jam'iyyun adawa a kasar sun caccaki Ganduje inda suka ce watakila ya na nufin APC ce matsalar zabe, cewar Channels TV.

Jami'yyar PDP a kasar ta ce dangane da maganan Ganduje hakan ya tabbatar da cewa APC ce matsalar zabe.

Sakataren yada labaran jami'yyar, Debo Ologunagba shi ya bayyana haka a jiya Litinin 22 ga watan Janairu.

Debo ya ce babban abin da ya kamata Ganduje ya yi shi ne neman afuwar 'yan Najeriya kan wadannan kalaman nasa.

Martanin jam'iyyun adawa ga Ganduje

Ya ce:

"Ya kamata Ganduje ya nemi gafarar 'yan Najeriya da kuma dana sani ba wai girman kai ba.
"Wannan kalaman ya tabbatar da cewa duk wata matsalar zaben daga jami'yyar APC ta ke zuwa.
"Jiga-jigan jam'iyyar APC a baya duk sun fadi abubuwa da ke tabbatar da haka, yanzu shugaban jam'iyyar ya kara tabbatarwa."

Kara karanta wannan

Kano: Dattawan APC a jihar sun shawarci Tinubu kan korar Ganduje, sun bayyana matsayarsu

Har ila yau, jami'yyar NNPP ta ce Ganduje ne babban matsalar dimukradiyya a kasar, cewar Daily Trust.

Sakataren yada labaran jami'yyar, Yakubu Shendam ya ce abin takaici Ganduje ya san shi ne matsalar dimukradiyya amma ya na zargin 'yan siyasa.

Ganduje na tsaka mai wuya

Kun ji cewa wasu matasan APC sun bukaci Shugaba Tinubu ya kori Abdullahi Ganduje.

Matasan sun yi wannan kiran ne da zargin cewa shugaban jam'iyyar ya gaza kawo jihar Kano a zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel