Kwamishinan Ganduje Ya Nemi Korar Mutum 3 a APC, a Dauko Kwankwaso Daga NNPP

Kwamishinan Ganduje Ya Nemi Korar Mutum 3 a APC, a Dauko Kwankwaso Daga NNPP

  • Muazu Magaji Dansarauniya ya kawo shawarar ayi wa jam’iyyar APC garambawul a reshen jihar Kano
  • Tsohon kwamishinan ayyukan na Kano ya zargi wasu shugabanni da kawo masu rashin nasara a kan NNPP
  • Dansarauniya zai so jam’iyyar APC ta shigo da Rabiu Kwankwaso da Kwankwasiyya da ke da mulki

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Muazu Magaji Dansarauniya ya shaida cewa bai halarci taron manyan APC ba, wanda yace an yi a jihar Kano a yau Alhamis.

‘Dan siyasar ya tofa albarkacin bakinsa a Facebook, ya nuna bai goyon bayan shugabannin da ke rike da APC ta reshen Kano.

Kwamishinan Ganduje
Abdullahi Ganduje da Gwamnan Kano Hoto: Salihu Tanko Yakasai da Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ganduje ya isa jihar Kano, zai gana da masu ruwa da tsaki kan batun sasantawa da Kwankwaso

Kano: Sai an kori mutum 3 a APC

"Ba mu je taron APC ta mutum uku ba a kano Yau! Domin mu bamu yadda da Shugabancin ta ba!
Amma muna mika sahawarwari online don dubawa da yin nazari yayin taron a yau!"

- Muazu Magaji

Shawarar Dansarauniya ga APC da Ganduje

Sai dai duk da rashin halartarsa, tsohon kwamishinan ayyukan yace za su cigaba da bada gudumuwa ga jam’iyyar ta kafar yanar gizo.

Daga cikin shawarwar farko da ya bada shi ne dole ayi waiwaye a kan wasu kalamai da shugabannin APC suka rika yi a lokutan baya.

Da alama Injiniya Muazu Magaji yana magana ne a kan Abdullahi Abbas wanda yake jagorantar jam’iyyar APC ta reshen Kano tun 2018.

Tsohon kwamishinan da yake ta ruwan maganganu a shafin Facebook ya zagi mutane uku da jawowa jam’iyya mai-adawa cikas.

“Allah ya bar mu sai lokacin da ya ga dama ya yi mana hukunci! Idan muna son yin wani tasiri ko bayan merger to sai mun nemi gafarar fushin Allah a APC!”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu ya dage zai daurawa jam'iyyar APC da NNPP auren dole a Kano

- Muazu Magaji

Su wanene suka cuci APC a Kano?

A cewarsa wadannan mutane uku suka jawo wankin hula ya kai APC dare a 2019, a karshe kuma NNPP tayi masu lilis a zaben 2023.

Idan aka yi waje da wadannan jagorori, Dansarauniya yace APC za ta zama jam’iyyar al’umma, sai kuma a hada-kai da NNPP mai mulki.

Kwankwaso ya dawo APC

Bayanan jigon na APC a Facebook sun nuna ya goyi bayan a hadu da ‘yan Kwankwasiyya domin kara karfi, yace ba yau aka fara ba.

Shekaru kafin a kafa a shiga NNPP, Rabiu Kwankwaso da mabiyansa su ne rike da APC.

Isowar Ganduje Kano a makon nan

A jiya ne rahoto ya zo cewa Abdullahi Umar Ganduje domin yin taro da 'yan APC.

Zuwa yanzu dai Abdullahi Ganduje ya je gidajen Sheikh Yusuf Ali, Sani Lawal Kofar Mata da Alhaji Bello Maitama ya yi masu ta’aziyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel