Abubuwa 10 da Za Su Faru da NNPP da APC Idan Abba, Kwankwaso Suka Sauya-Sheka

Abubuwa 10 da Za Su Faru da NNPP da APC Idan Abba, Kwankwaso Suka Sauya-Sheka

  • Abdullahi Umar Ganduje ya fito karara yana kira ga Abba Kabir Yusuf ya sauya-sheka daga NNPP
  • Shugaban APC na kasar yana so gwamnan jihar Kano da mabiyansa su dawo jam’iyya mai mulki
  • Idan ‘yan Kwankwasiyya da NNPP suka shigo APC, abubuwa za su iya rikida a siyasar Kano da kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Legit tayi hasashe yadda abubuwa za su koma idan gwamnatin NNPP ta narke a APC kamar yadda Abdullahi Ganduje ya nema.

Kano NNPP
Shugabannin APC da Gwamnan Kano Hoto: Salihu Tanko Yakasai, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ya siyasar Kano da kasa za ta koma?

1. Rushewar NNPP

Da zarar Abba Kabir Yusuf ya sauya-sheka daga NNPP, jam’iyya mai kayan marmari za ta zama ba ta da gwamnati ko guda a duk Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Jigo a NNPP ya yi zancen yiwuwar hadewar Abba, Kwankwasiyya da Ganduje a APC

2. Rasa ‘yan majalisun dokoki

Sauya shekar gwamna da uban gidansa, Rabiu Kwankwaso zai iya jawo NNPP ta rasa kujerun majalisar dokoki da take da su a Kano a Bauchi.

Watakila za a zama babu wata jam’iyya mara rinjaye kenan a majalisar dokokin Kano.

3. Rinjayen APC a majalisar tarayya

A hasashenmu, hakan yana nufin Sanatoci biyu da ‘yan majalisar wakilan tarayya daga jihohin Kano da Jigawa za su koma APC mai rinjaye.

Bayan haka dole irinsu Sanata Rufai Hanga da Aliyu Madaki su rasa mukaman marasa rinjaye idan suka yi tsalle daga NNPP mai kayan dadi.

4. Tazarcen Abba Gida Gida

Idan Kwankwasiyya ta amsa gayyatar shugaban APC, watakila ayi yarjejeniyar cewa Abba Kabir Yusuf zai nemi tazarce babu hamayya a zaben 2027.

5. Makomar Nasiru Gawuna

Shigowar Abba zai iya toshe duk wata kofar takarar Nasiru Gawuna a 2027. ‘Dan takaran na APC a zaben 2023 ya ga samu ya ga rashi a kotunan zabe.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje ya roki Abba Gida-Gida ya shigo jam’iyyar APC

6. Mukamai a gwamnatin Kano

Watakila narkewar NNPP a jam’iyya mai mulki ta haifawa APC da Gandujiyya kujeru da mukaman gwamnati karkashin jagorancin Abba domin a tafi tare.

7. Mukamai a gwamnatin tarayya

Baya ga Nasiru Gawuna, babu mamaki hadin gwiwar ta taimakawa ‘yan bangaren Kwankwasiyya samun wasu mukamai a gwamnatin Bola Tinubu.

8. Sababbin shugabannin APC a Kano?

Idan har ana so APC ta zama dangi daya, jagororin ‘yan siyasa za su bukaci a canza shugabannin jam’iyya na reshen Kano, wasu tun 2018 suke ofis.

9. Makomar Abdullahi Ganduje a NWC

‘Yan kwankwasiyya za su ji tsoron ba za su samu tikitin 2027 ba muddin Abdullahi Ganduje yana kujerarsa, watakila hakan ya kawo sauyi a NWC.

10. Ina za a kai Rabiu Kwankwaso?

Auren jam’iyyun APC da NNPP ya danganta ne da makomar Rabiu Musa Kwankwaso da rawar ganin da zai taka a matakin kasa na jam’iyya mai mulki.

Ganduje yana da nauyi a siyasar Kano?

Kara karanta wannan

Kwamishinan Ganduje ya nemi korar mutum 3 a APC, a dauko Kwankwaso daga NNPP

Mai ba gwamnan Kano shawara, Abba Dala yayi kaca-kaca da Abdullahi Ganduje, an ji labari ya zarge shi da kashe jam'iyyar APC a reshen Kano.

Abba Dala ya ce Dr. Ganduje bai san cancanta ba kuma Gandujiyya ta ci amanar Kawu Sumaila wanda a dalilin haka yace ya shiga tafiyar NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel