Kwankwasiyya
Maganar NNPP tayi wa APC taron dangi a Kano tayi karfi, Shekarau ya gujewa Gawuna. Malam Ibrahim Shekarau ya gujewa Nasiru Gawuna da ya je gidansa cikin dare.
Wasu 'Yan majalisar Kano, Abdullahi Iliyasu Yaryasa, (Tudun Wada), Muhammad Bello Butu Butu, (Tofa/Rimin Gady), da Kabiru Yusuf Ismail (Madobo) sun koma APC.
Wasu daruruwan ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC sun sauya-sheka zuwa NNPP a Zamfara. A halin yanzu NNPP ta na fara karfi musamman a jihohin Arewacin Najeriya gabanin 2023
Mun kawo sunayen wasu cikin wadanda suka yanki fam, suka fito neman takarar shugabanci daga Arewacin Najeriya bayan irinsu Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso.
Ibrahim Shekarau da Kawu Sumaila sun kammala shirye-shiryen ficewa daga APC. A karshen makon jiya Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya tsaida ‘yan takaran APC.
Inuwa Waya zai yaki Nasiru Yusuf Gawuna wajen samun takarar Gwamna a Kano a karkashin jam’iyyar APC. Waya ya ce sam ba zai fasa yin takara a zaben na 2023 ba.
Gwamnan Kano ya shiga takarar Sanata a Najeriya. Kujerar Maliya ta na yawo a iska, Dr. Abdullahi Ganduje zai nemi zaama Sanatan Arewacin jihar Kano a 2023.
Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya dauki mataimakinsa a matsayin ‘Dan takarar APC a 2023. Nasir Gawuna shi ne wanda ake tunanin zai rikewa APC tuta.
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, za ta samu gaggarumin nasara a zabukan shekarar 2023.
Kwankwasiyya
Samu kari