Rashin tsaro: Shugaba Buhari ya Sauka Daga mulki, ko a Tsige shi Inji Jam’iyyar NNPP

Rashin tsaro: Shugaba Buhari ya Sauka Daga mulki, ko a Tsige shi Inji Jam’iyyar NNPP

  • Shugaban jam’iyyar NNPP a Katsina ya kira taron zantawa da manema labarai a farkon makon nan
  • Sani Liti ya nemi Mai girma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ajiye shugabancin kasar
  • Liti ya nemi Majalisa ta tunbuke Shugaban kasar idan har yayi taurin kan rubuta takardar murabus

Katsina - Shugaban jam’iyyar NNPP na reshen jihar Katsina, Hon. Sani Liti, ya yi kira ga Mai girma Muhammadu Buhari ya gaggauta barin karagar mulki.

Daily Trust ta rahoto Honarabul Sani Liti yana mai kira ga shugaban Najeriyan ya rubuta takardar murabus, domin ya gaza kawo karshen matsalar tsaro.

Shugaban NNPPP ya kira taron manema labarai a ranar Litinin 25 ga watan Yuli 2022, ya bukaci Muhammadu Buhari ya sauka daga kujerar da yake kai.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya Bada Sabon Mukami, ya Maye Gurbin Wanda ya ba Minista a Kano

Da yake bayani a taron, Sani Liti ya ce a yau matsalar rashin tsaro ta addabi al’umma, tare da karin talauci da ake fama da shi a dalilin wasu manufofin tattali.

An rahoto Liti yana cewa rigingimun kabilanci sun yawaita game da kashe-kashe da kuma rashin gaskia da ya dabaibaye ko ina a karkashin mulkin Buhari.

NNPP ta bada shawara

Jam’iyyar adawar tayi kira ga gwamnatin tarayya ta sa dokar ta-baci a kan sha’anin tsaro, sannan a dauko hayar kwararru daga ketare da su taya kasar yaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari tare da Hafsoshin tsaro
Asali: UGC

Bugu da kari, shugaban na NNPP ya bada shawarar a dauki matasa miliyan daya a ba su horaswa na musamman ta yadda za su yaki ‘yan bindiga a kasar nan.

NNPP ta ce lamarin rashin tsaro ya yi kamari a jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara, Neja da Sokoto.

Kara karanta wannan

Na kadu: An kashe dan uwan shugaban PDP, Buhari ya sha alwashin daukar mataki, ya kakkausan martani

Majalisa ta dauki mataki

“Gwamnatin Buhari ta gagara inganta rayuwar ‘Yan Najeriya kamar yadda aka yi alkawari, sai ma ta tsumbula kasar cikin rashin gaskiya da wahala.
Idan har shugaban kasar ya ja kafa, ko ya ki yarda ya yi murabus, muna kira ga majalisa tayi amfani da tsarin mulki, ta ceci rai da dukiyoyin al’umma.”

Mutum 50, 000 sun mutu

“Ya kamata ayi bayani cewa daga shekarar 2015 zuwa yanzu, miyagun ‘yan bindiga sun kashe sama da mutanen Najeriya 50, 000.
Sannan an yi asarar Tiriliyoyin kudi da kadarori wajen biyan fansa a hannun masu tada kafar baya, ana sayen makamai da wannan kudin.”

Rashin tsaro a Zamfara

A baya an ji rahoto cewa akwai hikimar da ta sa Sarkin Birnin Yandoto ya zabi tsohon ‘Dan bindiga, ya ba shi babbar sarautar Sarkin Fulani.

Kakakin Masarautar Yandoto ya ce Ado Aliero ya tuba, kuma ya taimaka sosai wajen kawo zaman lafiya da hana ‘yan bindiga su kawo masu hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel