Kwankwaso ya yi karin-haske a kan ‘goyon bayan’ APC da Bola Tinubu a zaben 2023

Kwankwaso ya yi karin-haske a kan ‘goyon bayan’ APC da Bola Tinubu a zaben 2023

  • Rabiu Musa Kwankwaso yace bai hakura da neman zama shugaban kasar Najeriya a 2023 ba
  • Kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso ya fitar da jawabi na musamman ta bakin Muyi Fatosa
  • Fatosa ya ce ‘Dan takaran na NNPP bai janye ba, kuma sam bai yi wa Bola Tinubu mubaya’a ba

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanya cewa sun yi wa Asiwaju Bola Tinubu mubaya’a a zaben 2023.

A wata sanarwa ta musamman da ta fito daga kwamitin yakin zaben shugaban kasar, an tabbatar da cewa ‘dan takaran na jam’iyyar NNPP bai janye ba.

Sanarwar ta ce Rabiu Kwankwaso yana takarar zama shugaban kasa, kuma bai damu da rahotannin karyan da ke nuna yana goyon bayan Bola Tinubu ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Idan na rasa kujerar Buhari, kowa ma ya rasa, amma Tinubu ya samu

"Kwankwanso yana cigaba da samun goyon baya daga mafi yawan mutanen Najeriya.

Abin da Kwankwaso ya fada

Domin karin-haske, sanarwar ta fadi abin da Kwankwaso ya fada a hirar da ya yi da Dr. Reuben Abati na gidan talabijin Arise TV a game da Bola Tinubu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayani karara cewa: “Bola Tinubu aboki na ne na tsawon shekaru, da ba na takara, na bada shawarar a zabe shi."
Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a taron siyasa Hoto: @salisuyahayahototo
Asali: Facebook

Ba na yin siyasar gaba, dukkanninmu ‘yan takarar shugaban kasa ne, amma na fi cancanta.”

- Muyi Fatosa

Hadimin ‘dan takaran, Muyi Fatosa wanda ya fitar da wannan jawabi a Facebook, ya ce abin takaici ne a juya kalaman, ana cewa yana tare da Bola Tinubu.

A rika tantance labarai

“Kwamitin yana mai matukar karyata wannan rahoto na cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya bi Tinubu, tana kira ga mutane su rika tantance labarai.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Kwankwaso ya gamsu da hadin Tinubu da Shettima

“Kwamitin yana karfafawa masu ruwa da tsaki, ‘yan jam’iyya da magoya baya su yi watsi da wannan karya, su cigaba da goyon bayan wanda ya dace.”
“Mu na kara tabbatarwa mutanen Najeriya da dinbin magoya bayan Rabiu Kwankwaso a gida da waje cewa shi ne ‘dan takaran da za gwabza da shi.”

- Muyi Fatosa

Dalung ya ziyarci Kwankwaso

Mu na da rahoto an ga Barr Solomon Dalung wanda tsohon Minista ne a Najeriya a gidan Rabiu Musa Kwankwaso, ya je gaisuwar yawon sallah a Kano

Har yanzu ba mu da masaniyar ko ‘dan siyasar na jihar Filato ya shiga jam’iyyar NNPP mai alamar kayan dadi, duk da an gan shi dauke da jar hula.

Asali: Legit.ng

Online view pixel