Kasashen Duniya
A ranar Juma'a ne Majalisar Dinkin Duniya ta karbi wani korafi tare da neman ta binciki Gwamna Abba Kabir Yusuf, kan tashin tashinar da ake yi a jihar Kano.
Bayan kwashe shekaru 80 ana nema, rahotanni sun bayyana cewa an gano jirgin yakin da ya bace tun a lokacin Yakin Duniya na biyu. Warren Singer ne matukin jirgin.
Ma'aikatan jinya su yi wa mara lafiya addu'a laifi ne a kasar Ingila. An ruwaito cewa 'yar Najeriyar ta yi wa wani mara lafiya addu'a ne, shi kuma ya yi kararta.
A cewar asibitin a shafin Facebook sun yi amfani da fasahar IVF akan dattijuwar, kuma tana cikin koshin lafiya bayan haihuwar. Dattijuwar ta kafa tarihi a Afrika.
Sanatocin Arewa sun yi wani zama. su ka bukaci Bola Tinubu ya maidawa Nijar wutan da aka yanke, a bude filin jirgin sama, sannan Sojojin Nijar su bar mulki a 2025.
Fadar Shugaban kasa ta bada sanarwa a yau cewa Bola Tinubu zai kasar waje. Bola Tinubu zai tafi Dubai a kasar UAE ne domin halartar taron COP28 da za ayi.
Dokin zuciya ya ja wani ango ya kashe amaryarsa, kanwarta da surukarsa a ranar aurensu a lardin Arewa maso Yammacin kasar Thailand. Ya kuma harbi wasu hudu.
Kungiyar SERAP ta bukaci Bankin Duniya da ya dakatar da ba jihohin Najeriya rancen kudi kan zargin almubazzaranci. Ana bin jihohin bashin naira tiriliyan 9.17.
An samu fargabar yin juyin mulki a kasar Saliyo lokacin da wasu yan bindiga suka kai farmaki a wani barikin sojoji tare da kokarin kwace wajen ajiyar makamai.
Kasashen Duniya
Samu kari