An Gano Jirgin Yakin da Ya Bace Tun Lokacin Yakin Duniya Na II Bayan Shekara 80

An Gano Jirgin Yakin da Ya Bace Tun Lokacin Yakin Duniya Na II Bayan Shekara 80

  • Bayan kwashe shekaru 80 ana nema, rahotanni sun bayyana cewa an gano jirgin yakin da ya bace tun a lokacin Yakin Duniya na biyu
  • Matukin jirgin, Warren Singer ya bace tare da jirginsa a ranar 25 ga watan Agusta, 1943 yayin kai wani kazamin hari kan filin jiragen Italiya
  • Sai dai bayan shekaru 80, wata tawagar masu aikin su sun gano abin da ya yi saura daga jirgin, amma ba su iya gano gawar Singer ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

An gano wani jirgin sama na yaki da ya bace a wani hari mai ban tsoro da aka kai Italiya, kwanaki kadan kafin sojojin kawance su kai hari, wanda ya kawo karshen wani rikitaccen al'amari da ya faru tun Yakin DSuniya na biyu.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun halaka dan bindiga, sun ceto malamin addini da wasu mutum 2 a jihar arewa

Shekaru 80 da Yakin Duniya na II, an gano jirgin Warren Singer, kirar P-38.

A shekarar 1943 Singer ya tuka jirgin P-38 don kai wani mummunan hari ga abokan gaba.

Tsawon shekaru 80 bacewar jirgin P-38 ta zama kamar almara, wacce aka warware yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Warren Singer, wani matukin jirgin Amurka, ya bace tare da jirginsa mai lamba P-38 a ranar 25 ga watan Agusta, 1943, a lokacin da ya kai hari a filayen jiragen saman Italiya kusa da Foggia, a gabashin kasar.

An gano jirgin Warren Singer kirar P-38 a teku bayan shekaru 80
An gano jirgin yakin da ya bace tun lokacin Yakin Duniya na II bayan shekara 80. Hoto: Dave Clark/Pen News
Asali: UGC

Ko Warren Singer ya samu nasarar harin da ya kai?

Wannan harin da Singer ya kai ya samu gagarumar nasarar lalata jiragen abokan hamayya guda 65, amma an rasa jirge kirar P-38 guda bakwai.

Rahotanni sun bayyana cewa Laftanar Singer bai karasa inda zai yada zango ba aka neme sa aka rasa bayan an yi masa gani na karshe a Manfredonia, wani kauye a Gabashin Foggia.

Kara karanta wannan

Bidiyon zanga-zangar da ta barke a Kano kan zargin 'yan sanda sun kashe farar hula

Yanzu bayan shekaru 80, wasu masu aikin su, sun gano abin da ya yi saura daga jirgin Singer a nisan mita 12 (kafa 40) a kasan tekun Manfredonia.

Me ya faru da jirgin P-38 ya nutse a teku?

Singer wanda ya ke da shekaru 22 a wancan lokaci ya tafi ya bar matarsa Margaret, wacce ya aura watanni biyar kafin kai harin, rahoton jaridar The Sun.

An haifi diyarsu Peggy a cikin watan Janairu 1944, inda iyalansa su ke kallonsa matsayin wani gwarzo wanda ke cike da kyawawan mafarkai.

A cewar jaridar MailOnline a ranar Alhamis, masuncin da da ya gano jirgin, Fabio Bisciotti, ya ba da rahoton cewa jirgin yana nan cikin yanayi mai kyau.

A cewar rahotansa, jirgin ya fada ruwan ne sakamakon matsalar inji, inda kuma ya ke hasashen Singer ya fita daga jirgin amma ya nutse a cikin tekun.

An gano gawar Warren Singer?

Kara karanta wannan

Daga musayar magana: Ango ya kashe amaryarsa da surukarsa a ranar aurensu

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin Singer na P-38 shi ne jirgi daya tilo da ya bace a yankin, wanda ya sa aka tabbatar shi ne yanzu aka gano.

Duk da kokari na tawagar masu aikin su din, sun gaza gano abin da ya saura daga gawar Singer.

Masanin tarihi Steve Blake ya bayyana cewa an samu rudani a kan bacewar Singer, wanda aka manna sunansa a jerin wadanda suka bace a Tunisia.

Wutar lantarki: Ministan Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya albishir

A wani labarin, gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta sha alwashin kawo karshen duk wasu matsaloli da ke addabar fannin wutar lantarki, Legit Hausa ta ruwaito.

Ministan wutar lantarki Adelabu ya ce akwai tsarin da za su kaddamar da zai kawo tsayuwar wutar lantarki a birane da kauyukan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel