Sanatocin Arewa Sun Hadu, An Huro Wuta a Janye Takunkumi, a Maidawa Nijar Kasar Wuta

Sanatocin Arewa Sun Hadu, An Huro Wuta a Janye Takunkumi, a Maidawa Nijar Kasar Wuta

  • Sanatocin jihohin Arewacin Najeriya sun sake yin tir da yadda aka kakaba takunkumi a kan Nijar saboda juyin mulki
  • Abdul Ningi ya ce matakin da aka dauka saboda an hambarar da Mohammed Bazoum ya na azabtar da har ‘Yan Najeriya
  • Kungiyar Sanatocin ta bukaci a maida wuta, a bude filin jirgin sama, sannan Sojojin Nijar su kyale Bazoum ya sha iska

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kungiyar Sanatocin jihohin Arewa ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu ya maidawa kasar Nijar wutar lantarkin da aka yanke.

Sanatocin sun bukaci Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi wannan ne a matsayinsa na shugaban ECOWAS kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kwanaki 6 da dawowa Najeriya, Shugaba Tinubu zai lula kasar Larabawa gobe

ECOWAS
Bola Tinubu a taron ECOWAS Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Sojojin Nijar za su sauka nan da 2025?

Sanatocin yankin Arewa sun bukaci sojojin da su ka hambarar da gwamnatin Nijar su rage wa’adin da za su yi a kan mulki zuwa shekaru biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan majalisa sun sanar da duniya matsayarsu ne bayan wani taron gaggawa da su ka yi a majalisar tarayya karkashin jagorancin Abdul Ningi.

ECOWAS ta wahalar da Nijar da Najeriya

Sanata Abdul Ningi wanda ya karanto jawabin bayan taron ya ce takunkumin da aka kakabawa Nijar saboda juyin mulkin ya shafi kasar Najeriya.

Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawan ya ce ‘yan Najeriya da ke iyaka da Jamhuriyyar Nijar sun taggayara a dalilin matakin.

Matsayar Sanatocin Arewa kan juyin mulkin Nijar

"Mu na masu tir da juyin mulkin da sojoji su ke yi wa farar hula a Afrika. Sannan mu na kira ga sojojin Nijar su saki Mohammed Bozoum ya zauna a kasar da yake sha’awa.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri, Tinubu na da shirin ciyar da kasar nan gaba, shawarin minista ga 'yan Najeriya

Mu na so sojojin su tsara jadawalin shirin mika mulkin wanda bai zarce shekaru biyu ba.
A janye takunkumin da aka kakabawa Nijar saboda ‘yan Najeriya su na shan wahala a dalilin juyin mulki da takunkumin da ya biyo bayan shi."

- Abdul Ningi

Ningi: "Nijar da Najeriya 'yanuwa ne"

Premium Times ta rahoto cewa Sanatocin sun bukaci a bude filin tashin jirgin sama, kuma a bar Mohammed Bazoum ya je duk inda ya ga dama.

Baya ga kira ga Bola Tinubu, Ningi a madadin sauran Sanatocin ya fadawa mutanen Nijar cewa har yanzu su ‘yanuwa ne kuma abokan huldarsu.

Sojojin Nijar za su kashe Bazoum?

A watan Yulin bana aka tabbatar da cewa Mohammed Bazoum ya sauka daga mulki da karfin bindiga bayan shekaru kusan biyu a Jamhuriyyar Nijar.

Sojojin tawayen da su ka karbi mulki sun nuna muddin aka auko masu da yaki, za su iya kashe Mista Bazoum da ake neman dawo da shi kan kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel